Connect with us

Uncategorized

‘Yan hari sun kashe DPO ‘yan sanda a Jihar Edo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mahara da bindiga sun kai wa Ofishin jami’an tsaron ‘yan sanda da ke karamar hukumar Owan, a Jihar Edo hari.

An bayyana ga manema labarai da cewa harin ya faru ne a misallin karfe 8:00 na daren ranar Talata da ta gabata, a nan yankin Afuze, a karamar hukumar Gabashin Owan ta Jihar Edo, inda suka kashe DPO jami’an ‘yan sandan yankin da ofisoshi ukku da ke a kan tsaro a ranar.

Rahoto ta gabatar da cewa ‘yan harin sun kara isa ga Ofishin Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), har da kone kayakin zabe da ke a cikin ofishin.

“Mun ji ne kawai tashin harsasun bindiga a iska ba tare da sanin abin da ke gudana ba har sai da safiyar Laraba kamin muka gane da hakan” inji Mista Godwin Ikpekhia, wani mazaunin unguwar a bayanin sa da manema labarai.

“Sun kashe DPO jami’an tsaron ne hade da ofisoshi ukku a yayin da sauran suka riga da fita zuwa yawon tsaro a wajaje” inji shi.

Ya kara da cewa ‘yan harin sun lallace motar jami’an tsaron da aka faka cikin ofishin su.

Ga sunayan wadanda suka mutu sakamakon harin;

DPO jami’an tsaron, Supt. Tosimani Ojo, Sgt. Justina Aghomon, wata macce da cikin ta, Insp. Sado Isaac da kuma Cpl. Glory David.

An bayyana da cewa Kwamishanan jami’an tsaron yankin Edo, Mista Muhammed Danmallam, ya ziyarci wajen da abin ya faru, ya kuma kadamar da bincike akan abin.

Mista Danmallam ya furta da rantsuwa da cewa hukumar zata tabbatar da ganin cewa an kame wadanda suka aiwatar da wannan mumunar harin da kuma ganin cewa sun dauki matakai ta musanman akan hakan.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Kano sun fada da cewa “Aikin mu na kare yancin Al’umma ne, ba kisan kai ba”,  a wata bayani da suka yi lokacin zaben gwamnoni da ta gidan majalisar Jiha.