Labaran Najeriya
An bai wa Yusuf Buhari, yaron Shugaban kasar Najeriya takardan bautar kasa (NYSC)
Yusuf Buhari, Yaron shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya karbi takardan kamala bautar kasa (NYSC) ta shekara daya.
Naija News Hausa ta gane da cewa Yusuf ya kamala karatun babban jami’a ta biyu da ake kira (Master’s) ne tun watan Yuli, a shekarar 2016 da ta gabata.
Ko da shike ba a bayyana gari ko wajen da Yusuf yayi bautar kasan ba, amma muna da tabbacin cewa Yusuf ya karshe karatun sa ne tun shekaru da suka wuce a baya.
Bincike ya kuma nuna da cewa Yusuf da ‘yar uwar sa Zahra sun kamala karatun su ne a babban makarantar Jami’a ta kasar Turai da ake cewa ‘University of Surrey, Guildford’
Ga hoto a kasa yadda aka baiwa Yusuf takardan NYSC;
Mun tuna a Naija News a baya da cewa dan shugaban kasan, Yusuf tare da abokin cin mushen sa, Bashir Gwandu a baya sun yi hadari kan Babur a ranar 26 ga watan Disamba, shekarar 2017 da ta gabata a hanyar Gwarimpa ta babban birnin Tarayyar kasa, Abuja.
Mun kuma gane da cewa an tafi da Yusuf zuwa kasar waje a watar Fabrairu ta shekarar 2018, watau a lokacin da hadarin ya faru, don bashi kulawa ta gaske bayan da aka yi masa kulawar gaggawa a asibitin Cedarcrest da ke birnin Abuja, kamin tafiyar kasar Turai.
Karanta wannan kuma: Hukumar JAMB ta sanar da ranan da za a fara jarabawan JAMB ta shekarar 2019.