Uncategorized
An saki Hajiya Hauwa, Surukin Gwamnan Jihar Katsina da aka sace kwanakin baya
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wasu ‘yan hari da bindiga da ba a gane da su ba sun sace Hajiya Hauwa Yusuf da ke da shekaru 80, watau tsohuwar Binta Masari, daya daga cikin matan Aminu Masari, Gwamnan Jihar Katsina, a nan gidan ta da ke a Dandume, ta Jihar a makon da ta gabata.
Kakakin Jami’an ‘yan sandan Jihar, SP Gambo Isah ya bayyana ga manema labarai da cewa ‘yan harin sun saki Hajiya Hauwa Yusuf.
“An saki Hajiya Hauwa Yusuf. Ta dawo da cikakken lafiyar jiki ba tare da wata matsala ba, kuma mun bayar da ita ga iyalan ta. ” inji Isah wanda ya bayar da cewa sun yi wa Hajiya Hauwa bincike lafiyar jiki a yayin dawowar ta.
Hajiya Hauwa ta samu kubuta ne daga hannun ‘yan hari bayan kwana takwas da aka sace ta.
Ko da shike ba a bayyana yadda aka saki Hajiya Hauwa ko kuma wata kila jami’an ‘yan sanda suka yi gwagwarmayan gano ta. Amma dai jami’an ‘yan sandan na barazanar cewa suna bin wata liki don ganin cewa sun kame wadanda suka aiwatar da sace Hauwa.
Karanta wannan kuma: An Taras da Gawar wani dan makarantan UNIJOS a cikin wata Rijiya da ke a kewayan marantan jami’ar.