Connect with us

Uncategorized

Ba gaskiya ba ne, ban yi hadarin mota ba – Nasir El-Rufai

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya mayar da martani game da zancen cewa yayi hadarin mota.

Akwai jita-jita da ya mamaye yanar gizo ‘yan kwanaki kadan da suka gabata, da cewa Gwamna El-Rufai da direban sa sun yi hadarin mota har Gwamnan yayi mugun rauni sakamakon hadarin, a fadin mutane.

Gwamnan ya mayar da martani game da wannan jita-jitan a ranar Alhamis da ta gabata a cikin wata sanarwa da aka bayar ga Naija News da cewa ba gaskiya bane zancen.

“Ba gaskiya bane. Ba abin da ya faru dani ko direba na. jita-jitan shiri ce na ‘yan adawa na ganin cewa an tayar da hankalin al’ummar Jihar Kaduna” inji El-Rufai.

Gwamna El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata rekodin adiyo da aka bayar ga Naija News inda Gwamnan ya shawarci ‘yan Najeriya duka da yin watsi da jita-jitan da ya mamaye yanar gizo wanda masu radiyo mai jini ke yadarwa game da hadarin mota da yayi tare da direban sa.

“Abin da ke gaban mu itace kadamar da ci gaba da ayukan da zai inganta Jihar mu. Ba zamu bar masu jita-jita su lallace shirin mu ba, ko kuma jawo mana wata farmaki a Jihar” inji shi.

Gwamnan ya karshe da godewa ‘yan Najeriya da suka bada hankali da yi masa fatan alkhairi.

”Ina cikin koshin lafiya, kuma na gode ga Allah, zamu kuma ci gaba da samar da ci gaba a Jihar Kaduna”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Jam’iyyar PDP sun bayyana da cewa basu amince da sakamakon kuri’ar zaben Gwamnan Jihar Kaduna ba .