Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 15 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 15 ga Watan Maris, 2019

 

1. Kotun kara ta bayar da dama ga Shugaba Buhari don binciken kayakin zaben 2019

A ranar Alhamis da ta gabata, Kotun kara ta bayar da dama ga shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC da binciken kayakin da aka gudanar da zaben 2019 da ita.

Naija News Hausa ta gane da cewa jam’iyyar APC sun bukaci hakan ne bayan da dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci hukumar INEC a baya da bincike akan kayakin da aka yi amfani da ita wajen zaben 2019.

2. Ku dauki jagorancin Mabulbulan Man Fetur, Buhari ya gayawa NNPC

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni ga Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) da cewa su cigaba da jagorancin gidan Man Fetur mai Mabulbula goma shadaya ta (Shell Petroleum Development Company – SPDC).

Naija News ta gane da hakan ne a wata wasika da aka wallafa ga Daraktan Kamfanin Man Fetur ta NNPC, Dakta Maikanti Baru, a ranar 1 ga watan Maris, shekara ta 2019.

3. INEC: Ku fara kadamar da shirin kan zaben 2023, Farfesa Mahmood ya gayawa ‘yan Majalisu

Shugaban Hukumar Gudanar da Zaben Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya shawarci sanatocin Najeriya da cewa su fara kadamar da shiri akan zaben shekarar 2023, da bincike akan dokar zaben kamin lokacin ya gabato.

Farfesa Yakubu ya gabatar da hakan ne ga sanatocin a wajen hidimar mika takardan komawa ga kujerar mulki ga sabbin sanatocin kasar Najeriya da hukumar ta gudanar a birnin Abuja, ranar Alhamis da ta gabata.

4. Kotu ta hana Hukumar INEC da gudanar da zaben karo ta biyu a Jihar Adamawa

Kotun koli ta Jihar Adamawa ta hana hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) da kadamar da zabe a Jihar. Kamar yadda hukumar INEC ta gabatar a baya da cewa zasu kadamar da zabe ta karo biyu a jihohin kasar Najeriy a wajajen da aka samu matsalar rashin amincewa da sakamakon zabe da wasu matsaloli kuma, a ranar 23 ga watan Maris ta gaba.

Kotun ta gabatar da umarnin ne daga bakin Alkali Abdulaziz Waziri.

5. Hukumar INEC ta mika takardan mulki ga ‘yan Gidan Majalisa da suka lashe zaben 2019

A ranar Alhamis, 14 ga watan Maris da ya gabata, Hukumar kadamar da zaben kasa (INEC) ta mika takardan shugabanci ga ‘yan gidan majalisa da suka lashe kujerar Sanata a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da aka yi a Jihohin kasar Najeriya.

Rahoto ya bayar da cewa wadanda sunan su ya kasance a kan yanar gizon hukumar ne kawai aka ba wa takardan shugabancin.

6. Gidan Majalisa ta gabatar da ranar da zasu bada rahoto akan albashin ma’aikatan kasa

Gidan Majalisar Dattijai sun gabatar a zaman tattaunawa da majalisar suka yi ranar Laraba da ta gabata da cewa zasu mikar da rahoton su akan sabon tsarin albashin ma’aikatan kasa a ranar Talata ta mako na gaba.

Majalisar ta gabatar ne da hakan a jagorancin shugaban gidan majalisar, Sanata Bukola Saraki.

7. Kotu ba ta isa ta hana mu kadamar da zabe ba a Jihar Adamawa – inji hukumar INEC

INEC, Hukumar kadamar da zaben kasar Najeriya, a ranar Alhamis da ta wuce sun furta da cewa umarnin kotun koli ta Jihar Adamawa bai isa ya hana su kadamar da zaben ranar 23 ga watan Maris ba a Jihar da sauran Jihohin kasar da aka samu matsalar zabe a baya.

Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa hukumar INEC ta dakatar da zabe a wasu Jihohin kasar sakamakon wasu matsaloli da aka samu, kamar yadda hukumar ta gabatar.

8. Ba gaskiya ba ne, ban yi hadarin mota ba – Nasir El-Rufai

A ranar Alhamis da ta gabata, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya mayar da martani game da jita-jitan da ya mamaye yanar gizo da cewa yayi hadarin mota.

“Ba gaskiya bane. Ba abin da ya faru dani ko direba na. jita-jitan shiri ce na ‘yan adawa na ganin cewa an tayar da hankalin al’ummar Jihar Kaduna” inji El-Rufai a cikin wata sanarwa da aka bayar ga Naija News.

9. An tsige sunan Okorocha daga sunayan Sanatocin Kasa

Hukumar Gudanar da zaben kasa, INEC a ranar Alhamis da ta wuce ta yi hidimar mika takardan koma ga mulki ga sanatocin kasar Najeriya a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar kasa.

Naija News Hausa ta gane da cewa hukumar INEC ta tsige sunan Gwamna Rochas Okorocha daga tsarin sunayan sanatoci da aka ba wa takardan koma ga kujerar Sanata a kasar.

Ka samu cikakken labaraun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa