Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 18 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 18 ga Watan Maris, 2019

 

1. Hadaddiyar kasar US ta yaba wa Buhari ga yaki ta cin hanci da rashawa

US ta yaba wa shugaba Muhammadu Buhari da rage karfin cin hanci da rashawa a kasar Najeriya cikin tsakanin shekaru hudu akan mulkin kasar.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da kara bashi lokaci kadan don cika gurin sa ga kasar Najeriya.

2. Karya ne, ban janye daga Jam’iyyar PDP ba – Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya karyace jita-jita da ya mamaye layin yanar gizo na cewar ya janye daga jam’iyyar PDP da kuma janyewa  daga hidimar siyasa.

Jonathan ya mayar da martani akan wannan batun a wata sanarwa daga bakin mai bada shawara ga tsohon shugaban ta fannin labarai, Ikechukwu Eze, da cewa ba gaskiya ba ne tsohon shugaban bai janye daga jam’iyyar PDP ko kuma hidimar siyasa ba.

3. Ina cikin tsanancin game da zancen koma wa jam’iyyar APC – inji Gbenga Daniel

Gbenga Daniel, Tsohon daraktan gudanar da hidimar neman zabe ga dan takaran shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana da cewa mabiya bayan sa da masoya  na tsananta masa da zancen komawa jam’iyyar APC. “Masoya na sun tsananta mani da bukatar in koma ga jam’iyyar APC” inji shi.

Naija News ta gane da wannan rahoton ne a bayan kwana daya da Mista Daniel ya gabatar da janyewar sa daga jam’iyyar PDP da kuma matsayin sa a jam’iyyar.

4. Ihedioha bai da fasahan da zai jagoranci jihar Imo – inji Okorocha

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya fada da cewa sabon gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya kasa ga hikima ko fasahan da zai iya jagorancin jihar da ita.

Naija News ta gane da zancen ne a yayin da Okorocha ke mayar da martani game da zargin da sabon gwamnan Jihar ke yi na cewar an cire kudi kimanin biliyan N17b daga asusun Jihar bayan zaben gwamna da aka yi a Jihar.

5. Buhari ba zai kafa baki ba ga hidimar sauran zabannin a Jihohi – inji shugabancin kasa

Shugabancin kasa ta bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai kafa bakin sa ko nuna kulawa ga zaben sauran jihohin kasa, ko kuma bada umarni ga hukumar gudanar da zaben kasar (INEC) ba, ko hada makirci ga zaben don taimaka wa jam’iyyar APC.

Shugabancin kasar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka bayar ta wurin Garba Shehu, babban mataimaki ga yadda labarai ga shugaban kasa a ranar Lahadi da ta gabata.

6. Hukumar INEC tayi bayani akan sauran zaben Gwamnoni ta ranar 23 ga Maris a Jihar Adamawa

Hukumar Kadamar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC) a ranar Lahadi da ta gabata sun bayyana da cewa zaben gwamnonin da za a yi ranar 23 ga watan Maris a Jihar Adamawa zai kasance ne a kananan hukumomi 14 a Jihar.

Kasim Gaidam, the Resident Electoral Commissioner in the state, said the election would be conducted in 29 Wards (Registration Areas) and 44 Polling Units where over 40,000 votes were earlier cancelled in the recent governorship selection.

7. Zamu kame ‘yan ta’addan Jihar Kaduna – Hukumar ‘Yan Sanda

Hukumar Jami’an ‘yan sandan Jihar Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata sun yi barazanar cewa zasu kame ‘yan ta’addan da ke kai hari a yankunan Jihar Kaduna. Musanman wadanda suka kai hari ga kauyan Nandu ta karamar hukumar Sanga.

Yakubu Sabo, Mai yadda labarai ga jami’an tsaron yankin ya bayar ga manema labaran NAN da cewa hukumar tsaron ta watsar da jami’an tsaro a yankin da aka kai harin, “An kuma kai wadanda suka mutu da  wadanda suka samu raunuka a asibiti” inji shi.

8. Jam”iyyar PDP na zargin Okorocha da cire kudi daga asusun Jihar Imo

Jam’iyyar PDP ta Jihar Imo sun zargi tsohon gwamnan Jihar, Rochas Okorocha da cire kudi kimanin naira biliyan N17bn daga asusu hudu ta Jihar, bayan kwana ukku da aka kamala zaben gwamnoni a Jihar.

“Okorocha ya cire kudi naira biliyan N17bn ne don amfanin kansa” inji ‘yan Jam’iyyar.

9. ‘Yan Hari da bindiga sun sace wani Malamin Gargajiya a Jihar Edo

Wasu ‘yan hari da makami da ba a san da su ba a Jihar Edo sun sace malamin gargajiyan da ke a karamar  hukumar Ikpoba-Okha, Mista Godwin Aigbe.

An gabatar a rahoto da cewa ‘yan harin sun fada wa fadar malamin ne a ranar Asabar da ta gabata inda suka sace mutumin da sassafiya.

 

Ka sami cikakkun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button