Connect with us

Uncategorized

‘Yan hari da makami sun sace wani Sarki a Jihar Edo

Published

on

at

advertisement

A ranar Asabar da ta gabata, ‘yan hari da makamai sun sace, Godwin Aigbe, sarki da ke shugabancin yankin Enogie ta Ukhiri da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha, a Jihar Edo.

Kamar yadda aka bayar ga manema labarai, ‘yan harin da kimanin su biyar dauke da makami, sun hari fadar sarkin ne a safiyar ranar Asabar da ta gabata, inda suka sace sarkin a yayin da suke harbe-harben bindiga a sama a lokacin da suke aiwatar da harin.

Mazaunin shiyar sun bayar ga manema labarai da cewa, “yan harin sun haska wa motarsu wuta bayan da suka sace sarkin, suka kuwa tafi da daya daga cikin motar sarkin a guje suka bar fadar”

Rahoto ta bayyana da cewa sarkin, Godwin Aigbe, wani tsohon jami’in tsaron ‘yan sanda ne da yayi ritaya daga tsaron kasar ‘yan shekaru da suka gabata, ya kuma hau kujerar sarkin yankin don maye gurbin tsohon sa da daman ke kan kujerar kamin ya mutu.

Chidi Nwabuzor, Kakakin yada yawun ‘yan sanda yankin ya bayyana ga manema labarai da cewa an watsar da jami’an tsaro a ko ta ina don neman kame wadanda suka sace sarkin da kuma ribato ransa.

Mun sanar a baya a Naija News Hausa da cewa wasu ‘Yan hari da bindiga sun kashe DPO ‘yan sanda a Jihar Edo, sun kuma haska wa Ofishin hukumar INEC da wuta.

Karanta wannan kuma: ‘Yan hari da makami sun saki Hajiya Hauwa, Surukin Gwamnan Jihar Katsina da aka sace kwanakin baya