Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari sun kashe wani Kwamandan Sojojin Najeriya a Jihar Bauchi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya sun yi sabuwar rashi a yayin da ‘yan hari da makami suka kashe daya daga cikin kwamandan sojojin kasar a Jihar Bauchi.

‘Yan hari da bindiga a yau Litinin, 18 ga watan Maris, 2019 sun kashe Col. Mohammed Barack, Kwamandan rukunin ‘Garrison Commander, 33 Artillery Brigade of Nigerian Army da ke barikin Shadawanka, a nan Jihar Bauchi.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wasu ‘Yan hari da bindiga sun kashe DPO ‘yan sanda a Jihar Edo, sun kuma haska wuta ga Ofishin hukumar INEC da ke a yankin.

Wannan mugun al’amari na mutuwar Col. Mohammed ya sanya rundunar sojojin Jihar Bauchi da sojojin kasar cikin wata yanayin bakin ciki da kaito.

Rahoto ta bayar da cewa ‘yan harin sun kashe Kwamandan ne ranar Lahadi da ta gabata a yayin da yake tukin babur da kansa a hanyar da ta bi daga Bauchi zuwa Jos, a dawowar sa daga Jihar Kaduna.

Ko da shike ba a gane ainihin ko harin ta musanman bace ko kuma kwamandan ya fada ne a hannun ‘yan hari da ke kan hanya.

Naija News ta gane da cewa Kwamandan mutumin Kano ne, an kuma bayyana da cewa ana akan shirin don zuwa yin zana’izar sa a Kano a cikin lokaci.

“Ku zo nan a rukunin sojojin don ana kan bincike akan lamarin, ba zani iya bada wata rahoto ba akan layi cikin wannan hali da ake ciki ba tare da na sanar ga Kwamanda na ba” inji Kakakin yada yawun rundunar sojojin Bataliya na 33 Artillery Brigade, Major Yahaya Nasir Kabara, a bayanin sa da manema labaran Punch ranar Lahadi da ta gabata.

Karanta wannan kuma: Ku zo mu hada hannu mu gyara Jihar Kaduna, inji Gwamna Nasir El-Rufai