Connect with us

Uncategorized

Zamu kame ‘yan ta’addan Jihar Kaduna – Hukumar ‘Yan Sanda

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an ‘yan sandan Jihar Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata sun yi barazanar cewa zasu kame ‘yan ta’addan da ke kai hari a yankunan Jihar Kaduna. Musanman wadanda suka kai hari ga kauyan Nandu ta karamar hukumar Sanga.

Yakubu Sabo, Mai yadda labarai ga jami’an tsaron yankin ya bayar ga manema labaran NAN da cewa hukumar tsaron ta watsar da jami’an tsaro a yankin da aka kai harin, “An kuma kai wadanda suka mutu da  wadanda suka samu raunuka a asibiti” inji shi.

“An kuma kafa hadaddiyar hukumar tsaro ta ‘yan sanda da sojoji don tabbatar da tsaro a yankin da kuma zamar da bin doka ga al’ummar Jihar”

Mista Sabo ya kara da cewa kwamishanan jami’an tsaron yankin, Ahmad Abdurrahaman, ya nuna bacin rai da harin da kuma isar da gaisuwar ta’aziya ga iyalan wadanda abin ya faru da su.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘Yan hari da bindiga sun kashe kimanin mutane 22 a Birnin Gwari, ta Jihar Kaduna

Mista Abdulrahaman ya shawarci jama’ar yankin da janye wa kokarin mayar da harin da ake kai wa ga yankin.

“Kada ku yi kokarin daukar doka a hannun ku, ku bar hukuma ta dauki matakin da ya dace”

Kwamishanan ya gabatar ne da wannan akan harin da ‘yan ta’adda suka aka kai ga kauyan Nandu ranar 16 ga watan Maris, a inda suka kashe kimanin mutane 9 da raunana mutane 2 da lallace gidan mutane.