Uncategorized
2019: Kada ku gabatar da sakamakon zaben Jihar Bauchi, Kotu ta gayawa INEC
Kotun koli ta Abuja, babban birnin Tarayya ta hana Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) da gabatar da sakamakon zaben Jihar Bauchi.
Kotun ta umurci hukumar INEC da dakatar da hidimar zaben Jihar Bauchi, musanman gabatar da rahoton zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris da ya gabata a Jihar.
An gabatar ne da hakan ga hukumar INEC a jagorancin Alkali, Inyang Ekwo, a ranar Talata (yau) akan wata kara da ake akan Jam’iyyar APC da Gwamnan Jihar, Mohammed Abubakar wadda ya bukaci hukumar INEC da dakatar da sanar da sakamakon kuri’un zaben Jihar, musanman, zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa hukumar INEC ta yi barazanar cewa Kotu ba ta isa ta hana su kadamar da zabe ba a Jihar Adamawa.
Alkali Inyang ya fada da cewa wanda ke kan shugabanci zai dakata daga shugabancin sa daidai bayan da aka gama karar da ke gaban kotun.