Labaran Najeriya
Ku gabatar da ni a matsayin Shugaban kasa, ko a warware zaben 2019 – Atiku
Dan takaran shugaban kasa daga jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci kotun kara da gabatar da shi a matsayin shugaban kasan Najeriya bisa ga zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu 2019, ko kuma a warware zaben.
“Ku gabatar da ni mai nasara ga zaben shugaban kasa ko kuma a warware zaben shugaban kasa ta ranar 23 ga watan Fabrairu 2019″ inji Atiku.
Dan takaran ya bayyana hakan ne a karar da ya mika a gaban kotun kara a birnin tarayyar kasa, Abuja ranar Litinin, 18 ga watan Maris da ya gabata. Inda Atiku ya kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari akan hidimar zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.
Mista Emmanuel Enoidem, Mai bada shawara ga Jam’iyyar PDP ta tarayya, ya bayar ga manema labarai da cewa jam’iyyar ta bukaci a yi watsi da sakamakon zaben shugaban ta watan Fabrairu akan zargin makirci da ya bayyana ga hidimar zaben a jihohin kasar.
“Mun riga mun shirya kimanin mutane 400 da zasu bada tabbacin shaida akan wannan zargin a kotun kara” inji shi.
“Ku kadamar da kara ta gaske da zai bayyana da kuma nuna da cewa kasar Najeriya na cikin jagorancin dimokradiyya” inji Segun Sowunmi, kakakin yada yawu ga hidimar zabe ga Atiku Abubakar.
“Ya kamata Kotun kara ta yi hukuncin da ya dace. Ta kuma kadamar da shari’ar da zai nuna da cewa kasar Najeriya ta saura akan shugabancin dimokradiyya”
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce “Ya kamata ne ace Dimokradiyya ya bayyana ra’ayin mutane, amma hakan bai kasance ba ga zaben ranar Asabar, 23 ga Watan Fabrairu“ 2019 da ta gabata.
Dan takaran ya fadi wannan ne a wata zaman tattaunawa da suka yi a birnin Abuja akan zancen sakamakon zaben shugaban kasa, ‘yan kwanaki kadan bayan zaben.