Connect with us

Labaran Najeriya

Manoman Jihar Gombe sun yaba wa shugaba Buhari da bayar da Tallafi

Published

on

at

advertisement

Manoman Shinkafa ta Jihar Gombe da suka karbi tallafi na noman shinkafa cikin ranin daga hannun gwamnatin tarayya wanda aka bayar a karkashin shirin ‘Anchor Borrower Programme’, sun bayyana murnan su da taimako da tallafi da aka basu wajen tafiyar da noman su ta rani a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Wasu daga cikin wadanda suka ci amfanin wannan shirin, sun bayyana da cewa gwamnatin tarayya ta rabar da buhunan taki hudu akan kowani ekar gona, an kuma hada masu da buhunan irin shinkafa ta zamani, fanfo da ake feshi da ita da kuma maganin feshi na amfanin eka daya.

Kungiyar Manoman Shinkafa da aka fi sani da likin (RIFAN) sun bayyana hakan ne ga manema labaran NAN da cewa shugabancin kasar ta taimaka masu sosai da hidimar wajen ganin cewa sun karbi tallafi na gudanar da noman rani ta shekarar 2019.

“Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta taimaka mana kwarai da gaske, musanman wajen ganin cewa mun samu girbi mai kyau ga noman mu ta bana” inji Malam Hamisu Ahmadu, daya daga cikin manoma da suka amfana da tallafin.

“Wannan shirin zai karfafa manoma kwarai da gaske. zai kuma taimaka da yaduwar hatsi garemu da kuma kasar Najeriya gaba daya”

“An bani tallafi na kayan aiki kan eka ukku. Na karba kuma nayi alkawari ga gwamnatin tarayya da cewa zan yi amfani da shi a hanya da ta dace” inji shi.

Abubakar Musa, wani daga cikin manoman, ya ce “Mun gode kwarai da gaske da wannan shirin. kowani manomi da yayi rajista ga RIFAN ya samu rabon sa kamar  yadda girman gonar sa ta ke. kuma ba wata makirci ga rabon kayakin aikin” inji shi.

“Wannan shiri zai karfafa tattalin arzikin kasar Najeriya kwarai da gaske, musanman yadda abin ya shafi karfafa matasa da yin aiki da kansu” inji Maryam Usman, daya daga cikin matan da aka ba wa kayakin noma daga RIFAN.

Karanta wannan kuma: Gonar ajiyar hatsi mai kimanin kudi naira Miliyan daya (N1m) ya kame da wuta