Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 19 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 19 ga Watan Maris, 2019

1. Ku gabatar da ni a matsayin Shugaban kasa, ko a warware zaben 2019 – inji Atiku

an takaran shugaban kasa daga jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci kotun kara da gabatar da shi a matsayin shugaban kasan Najeriya bisa ga zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu 2019, ko kuma a warware zaben.

“Ku gabatar da ni mai nasara ga zaben shugaban kasa ko kuma a warware zaben shugaban kasa ta ranar 23 ga watan Fabrairu 2019″ inji Atiku.

2. Wata babbar gini ta rushe a birnin Legas

Naija News ta samu rahoto da cewa an samu karin rushewar wata gini kuma a Jihar Legas a ranar Litinin da ta gabata.

Ginin da ke a unguwar Alakoro, mai lamba 57 a Legas Island ya rushe ne da tsakar ranar Litinin da ta gabata.

3. An taba takardan kasafin dukiya na – Onnoghen

Tsohon shugaban Alkalin Kotun Najeriya, Walter Onnoghen, ya bayyana da cewa an taɓa takardan kasafin dukiyan shi guda biyu da ya bayar ga Kotun shari’a a baya.
Onnoghen ya gabatar da hakan ne a ranar Litinin da ta gabata a nan birnin Abuja, da cewa an taɓa takardun da ya bayar ga kotun a shekara ta 2014 da 2016 da ta gabata.

4. Dalilin da ya sa bamu bayar da dama ga Atiku da don binciken kayan zabe – INEC

Hukumar Gudanar da Hidimar zaben kasar Najeriya (INEC), sun bayyana dalilin da ya sa basu bayar da dama ga Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa daga jam’iyyar PDP ba, ga binciken kayakin da hukumar ta gudanar da zaben shugaban kasa da ita ba.

Hukumar INEC a bayar da takardan komawa ga kan mulki ga shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa, Yemi Osinbajo.

5. Kotu ta bayar da dama ga EFCC don bincike akan Babachir Lawal

Kotun koli ta birnin Tarayya da ke a Maitama ta bayar da dama ga Hukumar EFCC don kara binbini akan karar tsohon babban sakataran gwamnatin tarayyar kasa, SGF Babachir Lawal tare da wasu mutane ukku.

Ka tuna da cewa hukumar ta kame Babachir ne hade da Hamidu Lawal, Sulaiman Abubaka da Apeh Monday a ranar 12 ga watan Fabrairun da ta gabata, akan wata zargi.

6. ‘Yan hari da makami sun kashe kwamandan Sojoji a Jihar Bauchi

Rundunar Sojojin Najeriya sun yi sabuwar rashi a yayin da ‘yan hari da makami suka kashe daya daga cikin kwamandan sojojin kasar Najeriya a Jihar Bauchi.

‘Yan hari da bindiga a ranar Litinin, 18 ga watan Maris, 2019 da ta gabata, sun kashe Col. Mohammed Barack, Kwamandan rukunin ‘Garrison Commander, 33 Artillery Brigade of Nigerian Army da ke barikin Shadawanka, a nan Jihar Bauchi.

7. Zamu ci gaba da gudanar da zaben Jihar Rivers – inji INEC

Hukumar kadamar da hidimar zaben kasa, INEC ta bayar da cewa zasu ci gaba da gudanar da zaben Jihar har ga karshe.

Ka tuna da cewa Jihar na daya daga cikin Jihohin da hukumar ta dakatar da zaben su a baya zakan rashin amincewa da wasu zargi da suka taso.

8. Ba mamaki a rage Jam’iyoyin takarar kujerar mulki a kasar Najeriya – Falana

Mista Femi Falana (SAN), ya gabatar da cewa idan har hukumar INEC zasu gabatar da aikin su yadda ya kamata, musanman bisa ganin yadda hidimar zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 ya kasance; Lallai ya dace ta rage yawar jam’iyoyin takara a kasar zuwa jam’iyya goma (10) kawai.

Ka sami cikakku da karin labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button