Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojoji sun yi ganawar wuta da Boko Haram a Jihar Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya da ke yankin Adamawa sun yi ganawar wuta da ‘yan ta’addan a daren ranar Litini da ta gabata, sun kuma ci nasara da yaki da ‘yan ta’addan.

Daraktan yada labarai ga rundunar sojojin, Col Sagir Musa ya bayar ga manema labarai da cewa rundunar bayan wata kirar gaugawa aka samu daga ‘yan bangan da ke kauyan Maikadiri da cewa sun gane da motsin ‘yan ta’adda a kan hanyar yankin, “Sai Jami’an tsaron Batalia da ke a yankin Lassa a nan Borno suka tari ‘yan ta’addan a gaba missalin karfe 7:20 ta maraicen ranar Litini”

Col. Sagir ya kara da cewa sojojin sun fada wa ‘yan ta’addan da munsayar wuta har sai da suka kashe kadan daga cikin su. “Bayan da suka gane da cewa wutar ya musu karfi, sai sauran suka yi gudun hijira” inji shi.

Ko da shike ba a bayyana ko mutane nawa sojojin suka kashe ba, amma mun iya gane da cewa ‘yan ta’addan sun samu gujewa da ‘yan uwar su da aka kashe cikin duhun daren.

Sojojin sun samu ribato wasu makaman yaki daga ‘yan ta’addan, hade da motar ‘Ford’ guda daya, motar ‘Toyota Starlet’ biyu cike da abinci da kuma wata mota da ke cike da makamai.

Karanta wannan kumaZamu kame ‘yan ta’addan Jihar Kaduna – inji Hukumar ‘Yan Sanda.