Connect with us

Labaran Najeriya

An sace Sheikh Ahmad, Mai addu’a da kuma mabiya bayan Shugaba Buhari

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Mahara da bindiga sun sace Sheikh Ahmad Sulaiman, babban Malami da kuma masoyin shugaba Muhammadu Buhari.

‘Yan harin sun sace Sheikh Ahmad ne a yayin da yake kan komawa gidan sa a Jihar Kano bayan da kamala wata hidimar wa’azi da ya ke a Jihar Kebbi.

Sheikh Ahmad Sulaiman, sanannan babban Malamin Islam ne, kuma babban jigo ne da masoyin shugaba Muhammadu Buhari.

‘Yan hari da bindiga sun tari malamin ne a yayin da yake kan komawa ga iyalin sa a Kano, sun kuma bukaci a biya kudi kimanin naira Miliyan dari Ukku (N300m) kamin su sake shi, kamar yadda gidan jaridan PRNigeria suka bayar.

Naija News na da sanin cewa Sheikh Ahmad ya gudanar da hidimar du’a’i ga shugaba Muhammadu Buhari don samun nasara ga zaben kujerar shugaban kasa da aka yi a baya.

 

‘Yan harin sun bukaci sai an biya kudi naira miliyan dari ukku kamin su saki Sheikh. sun gabatar ne da hakan a wata adiyo da suka yi rikodin wadda gidan jaridan PRNigeria suka karba.

A cikin rikodin, ‘yan harin sun bayyana da cewa wani mai kudi, dan siyasa ne ya biya su kudi kimanin miliyan dari ukku da kuma yi masu alkawarin kara ga kudin idan har sun samu kame Sheikh Ahmad.

Sun fada da cewa Dan siyasan ya gabatar a garesu da cewa Sheikh Ahmad mugun dan ta’adda ne ta gaske.

“Bayan kame Sheikh Ahmad, mun bincike shi, ya kuma bayyana mana ko shi wani irin mutumi ne. Mun kuma gane da cewa zargin da dan siyasan ke yi da shi ba gaskiya bane. Mun iya gane da cewa Sheikh mutumi ne mai tsoron Allah, kuma malami ne na kwaran gaske” inji ‘Yan harin, a cikin rikodin da aka bayar.

“Amma, Ba zai dace ba da muyi watsi da kudi, naira miliyan dari ukku da dan siyasan ya riga ya biya mu. Zamu mayar masa da kudin don ba zamu iya aiwatar da aikin ba, bisa mun gane da cewa zargin ba gaskiya bace. zamu kuma saki Sheikh Ahmad” inji shugaban ‘yan ta’addan.

“Amma a wannan lokaci, mun bukaci ku (mutanen sa) da biyar mu kudin da dan siyasan ya biya mu, sa’annan mu sake shi. Zaku kuma biya mu kudin sayan man fetur da muka yi amfani da shi a yayin da muka dauke shi zuwa Jihar Kebbi”

“Idan kuma baku iya kun biya kudin ba, lallai ba zamu jinkirta ba da aiwatar da kisan Sheikh Ahmad”

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa ‘Yan Hari sun kashe wani Kwamandan Sojojin Najeriya a Jihar Bauchi.