Connect with us

Labaran Najeriya

APC/PDP: Na fiye Buhari da kuri’u Miliyan 1.6m ga zaben 2019 – Atiku

Published

on

Dan takaran kujerarar Shugaban Kasa daga Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi barazanar cewa ya fiye shugaba Muhammadu Buhari da kuri kimanin Miliyan daya da dari shidda (1.6m) ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da aka yi a baya, ranar 23 ga watan Maris.

Jam’iyyar PDP a jagorancin Atiku sun bayyana hakan ne a karar da suka wallafa akan Buhari ga zancen zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairu, 2019.

Atiku ya gabatar da karar ne mai falle 141 a ranar Litinin da ta gabata ga kotun kara.

Mun ruwaito a baya a Naija News kamar yadda hukumar INEC ta ta gabatar da cewa dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe tseren zaben ne da kuri’u 15,191,847 bisa Alhaji Atiku Abubakar mai kuri’u 11,262,978 daga jam’iyyar PDP.

Amma bisa bincike, kamar yadda Atiku da jam’iyyar PDP suka bayar, da cewa sakamakon zaben shugaban kasa da ke cikin kwanfutan hukumar INEC ya bayar da cewa Atiku na da kuri’u 18,356,732 fiye da yawar kuri’un da aka bayar a baya.

Karanta wannan kuma: Ba ruwan Buhari da sakamakon zaben ranar Asabar ta gaba – inji Shugabancin kasa