Uncategorized
Kash! Ibrahim Chatta Umar ya mutu
Naija News Hausa ta samu sabon rahoto da tabbacin mutuwar Etsu Patigi, Alhaji Ibrahim Chatta Umar bayan rashin lafiyar ‘yan kwanaki kadan.
Alhaji Chatta ya mutu ne daren ranar Talata, 19 ga watan Maris da ta gabata a garin Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya. Za a kuma yi hidimar zana’izar sa a yau Laraba, 20 ga watan Maris 2019 missalin karfe 2 tsakar ranar yau, kamar yadda al’adar Islam ta bayar.
“Wannan babban rashi ce kwarai da gaske. Alhaji Ibrahim Chatta mutumi ne mai ban girma, kuma mutumin adalci ne shi” inji Sarkin Ilorin da kuma shugaban kungiyar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji (Dr) Ibrahim Sulu-Gambari.
Sarkin ya gabatar da bayanin sa ne na ta’aziyya daga bakin babban sakataren kungiyar Shehu Alimi akan zamantakewar lafiyar kasa da ci gaba, Mallam Abdulazeez Arowona, a cikin wata sanarwa da ya gabatar bayan mutuwar Chatta.
Alhaji Sulu-Gambari ya kara da cewa Chatta mutum ne mai kwanciyar hankali da kuma kadamar da shirya zamantakewar lafiya ga al’ummar Jihar, musanman ma da duk yaran Nufawa da ke Jihar Kwara.
“Mutuwar Chatta abin takaici ne kuma da bakin ciki a garemu, gurbin sa kuma zai zama a sake a wannan lokacin” inji Alhaji Sulu.
Naija News ta gane da cewa Etsu Patigi na zaman mataimaki ne ga Sarkin Ilori, Alhaji Sulu-Gambari a shugabancin Sarakunan Jihar Kwara, kamin mutuwar sa.
“Ina rokon Allah da gafarta wa Chatta zunuban san, ya kuma sa ya kai ga shiga al-janatul firdaos, ya kuma yi ta’aziyya ga Iyalan sa da ya bari har ma mutanen Patigi hade da Nufawan kasar duka”
Wannan itace addu’ar Sarki Sulu-Gambari.
Karanta wannan kuma: Wuta kame gidaje da barin Iyalai 20 da rashin wajen kwanci da kayan zaman rayuwa