Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da bindiga sun ki sakin Malamin Zabe a Jihar Jigawa bayan karban N500,000

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Jumma’a da ta gabata, ‘yan hari da makami sun sace wani malamin zabe a Jihar Jigawa.

Mista John Kaiwa, Shugaban Ilimin Fasaha na Hidimar Zabe, ya bayyana ga manema da bada tabbacin cewa ‘yan harin sun sace Mahadi Hassan.

John ya bayar da cewa an sace Mahadi ne a hanyar Gwiwa ta Jihar Jigawa a ranar Jumma’a da ta wuce.

Rahoto ya bayar da cewa ‘yan harin sun ki sakin malamin zaben bayan da aka biya kudin da suka bukaci karba kamin su saki Mahadi.

Naija News na da sanin cewa ‘yan harin sun bukaci a biya su kudi kimanin naira dubu dari biyar (N500,000) kamin su sake shi.

Amma abin takaici hakan bai faru ba duk da cewa an biya kudin kamar yadda suka bukata.

“Maharan sun kira ni ne a ranar Asabar da ta gabata, da bukatar in biya kudi naira dubu dari biyar kamin su saki Mahahi” inji tsohon malamin zaben, Mahadi Kofar Wambai a bayanin shi da manema labarai.

“Sun bukace mu da biyar naiara dubu dari biyar 500,000 kamin su sake shi, ko kuma su kashe shi a rana ta biyu” inji shi.

Malam Wambai ya bayyana da cewa duk da biyar kudin da ‘yan harin suka bukaceshi da biya a ranar Lahadi da ta gabata, sun ki su saki Mahadi.

Hukumar gudanar da zaben kasa sun bada tabbacin hakan, da cewa lallai ‘yan hari sun sace malamin zaben su, Mahadi tun ranar Jumma’a da ta wuce a yayin da yake kan hanyar Kazaure.

Ana kan bincike da wannan al’amarin. Zamu sanar maku da yadda aka karshe a nan shafin.