Connect with us

Uncategorized

An kame ‘yan Sanda biyu da suka kashe Ofisan Civil Defence

Published

on

at

advertisement

Jami’an tsaron ‘yan sanda ta Abuja sun gabatar da jefa ‘yan sanda biyu da ake zargi da
kashe wani Ofisan hukumar tsaron kare Al’ummar kasa (Civil Defence) a kulle.
A wata sanarwa a baya, an ruwaito da cewa wasu ‘yan sanda sun kashe wani Ofisan hukumar
tsaro da kare yancin Al’umma, da aka fi sani da (Civil Defence) a nan shiyar Nyanya ta
babban birnin tarayyar kasa, Abuja.

An gabatar da kashe Ofisan jami’an tsaron yancin al’ummar kasar, Mista Ogar Jombo, a ranar
Laraba da ta gabata a gaban Matan sa da diyan sa.

An bayyana da cewa ‘yan sandan sun kashe Mista Jombo ne da zargin cewa ya karya dokar bin
hanya.

“Muna kan bincike akan lamarin. Ba zamu iya gane ainihin abin da ya jawo sanadiyar wannan
mugun abin ba a hakin yanzu, sai har mun kai ga kara bincike” inji bayanin kwamishanan
jami’an tsaron ‘yan sandan yankin Abuja, Bala Ciroma a bayanin shi da haddiyar kungiyar
manema labaran kasar Najeriya (NAN).

“Ko da shike mun gane akwai jayayya tsakanin Mista Jombo da ‘yan sandan, amma bamu da
tabbacin yadda abin ya fara tukunna” muna kan bincike.