Connect with us

Uncategorized

Hukumar INEC ta gabatar da yadda za ta kadamar da zaben Jihar Bauchi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Alhamis, 21 ga watan Maris, Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya (INEC) ta gabatar da yadda zasu tafiyar da zaben Jihar Bauchi.

Hukumar ta bayyana da cewa za a kadamar da da zaben gwamnoni ne a kananan hukumomi goma shabiyar (15) inda aka samu matsalolin zabe a baya. Kananan hukumomin kuma ta kunshi runfar zabe Talatin da shidda (36) inda za a gudanar da zaben.

Hukumar ta gabatar da hakan ne a wata zaman tattaunawa da suka yi, wanda aka bayar daga bakin Kwamishanan hukumar INEC na Jihar Bauchi, Malam Ibrahim Abdullahi, a nan Bauchi, cikin Gidan tattaunawa da Hedkwatan hukumar INEC ta Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban Hukumar INEC na tarayya.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Kotun Kara ta Jihar Bauchi ta hana Hukumar INEC da ci gaba da hidimar zabe a Jihar.