Connect with us

Uncategorized

Kalli yadda wani Matashi ya so ya kashe kansa akan Soyayya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta samu rahoton wani matashi da ke kokarin kisan kansa a Jihar Delta don yarinyar da yake soyayya da ita ta janye mashi da bin wani can.

An bayyana ne da cewa matashin ya ziyarci yarinyar ne makarantan jami’ar Fasaha ta Delta State Polytechnic, Otefe, inda yarinyar ke karatu don kokarin kara shigar zuciyar ta, amma sai yarinyar ta ki shi.

Da saurayin ya gane da cecwa yarinyar ta kii shi, ta nuna da cewa ba ta da muradin ci gaba da soyayyar da ke tsakanin su, sai saurayin ya fusata ya bar wajen.

yana barin wajen da fushi sai ya nufi cikin dajin da ke kusa da makarantar jami’ar don kashe kansa.

An bayyana da cewa matashin ya nemi fasassun kwallabe biyu, ya nufi daji da su, daga nan ya dingi yagar kansa da kwallaban don ya dauke ransa akan zafin soyayya da kuma fushin matakin da yarinyar ta dauka na yanke soyayyar da ke tsakanin ta da shi.

Wani da ke kan hanyar dajin ya ji kuwa da kukar saurayin, sai ya yi wuf da shiga dajin inda ya cinma saurayin cikin zubar jini sakamakon kwalban da ya yaga jikin sa da shi.
Ba don wannan mutumin da ya bi hanyar ba, watakila da saurayin ya mutu da zubar jini.