Connect with us

Uncategorized

Makiyayan Jihar Benue sun kashe mutane 10 da bindiga a yayin da suke barci

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An bayyana ga  Naija News Hausa da cewa wasu Mahara da ba a gane su ba sun hari kauyan Tser Uoreleegeb da ke a karamar hukumar Guma ta Jihar Benue a daren ranar Talata da ta gabata.

A bayanin mazaunan shiyar, Maharan sun fada wa kauyan ne a lokacin da mutane ke kwance a kofar gidan su da daren ranar Talata a kauyan, inda suka kashe rayuka goma (10) kamar yadda aka bayar a wata sanarwa.

“Sun harbe mutanen ne kuma suka fada daji da gudu bayan hakan don kada wani ya gane su.”

Mista Richard Shaor, Ciyaman na karamar hukumar Guma a bayanin sa da manema labarai ya bayyana da cewa yana tugumar da zargin cewa makiyayan yankin ne suka aiwatar da harin, kamar yadda aka san su da yin hakan.

Ya kara da cewa Makiyayan sun kashe wani a ranar Litini da ta gabata kamin harin da aka yi a daren ranar Talata a yankin Tser Uoreleegeb.

“Wadanda suka aiwatar da kisan mutun daya a yankin ne suka kara kadamar da kashin mutane goma a daren ranar Talata a nan yankin” inji Mista Richard.

Ya bayar da cewa an riga an bizine mutane goma da ‘yan harin suka kashe, kamar yadda mutanen kauyan suka bukace su da hakan.

Kwamandan Rundunar Sojoji ta ‘Operation Whirl Stroke, Maj Gen Adeyemi Yekini, ya bayyana da cewa suna kan bincike game da harin.

Malama Catherine Anene, Kakakin yada yawun jami’an ‘yan sanda Jihar ta bayar da tabbacin harin, kuma ta fada da cewa ta gano gawaki biyar a lokacin da ake zana’izar su a makabartan da ke a kauyan.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘Yan Hari da bindiga sun ki sakin Malamin Zabe a Jihar Jigawa bayan da suka karbi kudi naira dubu dari biyar (N500,000) daga Iyalin sa.