Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 21 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 21 ga Watan Maris, 2019

1. Dalilin da ya sa nasarar Buhari ba zai dade ba – Sanata Saraki

Shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya gabatar da cewa nasarar shugaba Muhammadu Buhari ga zaben kujerar shugaban da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu a shekarar 2019 ba zai dade ba.

Saraki ya gabatar da hakan ne a zaman tattaunawa da yayi da Kwamitin Manyan Shugaban Tarayyar kasar Najeriya (NEC) a ranar Laraba da ta gabata, a nan birnin Abuja.

2. Jam’iyyar PDP tayi zaman tattaunawa

A ranar Laraba, 20 ga watan Maris da ta gabata, Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) sun yi zaman tattaunawa ta Kwamitin Manyan Shugabannin Kasa a birnin Abuja.

Naija News ta gane da cewa shugaban Sanatocin Najeriya, Bukola Saraki hade da manyan Jam’iyyar sun halarci zaman.

3. Karya ne, Ban janye daga jam’iyyar PDP – Jimi Agbaje

Dan takaran kujerar Gwamnan Legas daga jam’iyyar PDP, Jimi Agbaje ya karyace jita-jitan cewa ya janye daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Naija News ta gane da cewa zancen ya mamaye yanar gizo ne ranar Talata da ta gabata, bayan da aka gabatar da dan adawan sa Babajide Sanwo-Olu daga jam’iyyar APC a matsayin mai nasara ga kujerar Gwamnan Jihar.

4. Gidan Majalisar Dattijai sun rattaba hannu ga kudin ma’aikatan kasa

Shugaban Sanatocin Najeriya, Bukola Saraki, a ranar Laraba da ta gabata ya rattaba hannu ga dokar biyan kankanin kudin ma’aikatan kasa na naira dubu 30,000.

Mun tuna a baya da cewa kungiyar ma’aikatan kasa sun bukaci gwamnatin tarayya da biyar ma’aikata kankanin albashi na naira dubu 30,000.

5. Buhari ba zai iya biyar bukatar ‘yan Najeriya ba – inji Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya gabatar da cewa shugabancin Muhammadu Buhari ba zata iya cika gurin ‘yan kasan Najeriya ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Obasanjo ya ce “Atiku ba Almasihu bane, amma zai fi Buhari iya shugabanci kwarai da gaske”

6. Na fiye Buhari da kuri’u Miliyan 1.6m – inji Atiku

Dan takaran kujerarar Shugaban Kasa daga Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi barazanar cewa ya fiye shugaba Muhammadu Buhari da kuri kimanin Miliyan daya da dari shidda (1.6m) ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da aka yi a baya, ranar 23 ga watan Maris.

Jam’iyyar PDP a jagorancin Atiku sun bayyana hakan ne a karar da suka wallafa akan Buhari ga zancen zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairu, 2019.

7. PDP: INEC sun rage kuri’u na ga zaben ranar 23 ga Watan Fabrairu 2019 – Atiku

Dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar da sakamakon kuri’un zaben shugaban kasa kamar yadda take a kwanfutan hukumar gudanar da zaben kasa (INEC).

A fadin sa “Hukumar INEC sun rage kuri’u na daga kwanfutan su ga sakamakon zaben jihohi 31 ta kasar da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu”

8. Jam’iyyar APC na zargin PDP da shigar kwanfutan Hukumar INEC

Yekini Nabena, Babban sakataren yada labarai ga jam’iyyar APC, na zargin dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP da shigar kwanfutan hukumar INEC don kara kuri’un jam’iyyar ga zaben 2019.

Nabena ya bayyana hakan ne don mayar da martani ga zancen da jam’iyyar PDP da Atiku ke yi na cewar dan takaran ya fiye shugaba Muhammadu Buhari da kuri’u ga zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019.

9. Nnamdi Kanu ya karbi kudi daga hannun Atiku – inji Annabi Anthony

Wani Annabi mai suna Anthony Nwoko da ke zama a Jihar Enugu ya zargi shugaban kungiyar ‘yan Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da karban kudi daga dan takaran shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Nwoko ya bayyana da cewa Nnamdi Kanu ya karbi kudi ne daga hannun Atiku daren washegarin ranar zaben shugaban kasa da aka yi a baya.

10. Bani da wata shirin kadamar da makirci ga zaben Jihar Kano – Tinubu

Babban shugaban Jam’iyyar APC ta tarayya, Tinubu, ya karyace zancen jita-jita da ya mamaye yanar gizo da cewa yana da shirin kadamar da makirci ga zaben kujerar Gwamna ta Jihar Kano don taimaka wa Abdullahi Ganduje da cin nasara.

Naija News ta gane da wannan bayanin ne daga bakin Tunde Rahman, Mai bada shawarwari ga Tinubu.

Ka samu cikakken labaran Najeriya daga shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button