Labaran Najeriya
PDP: Kalli Sakamakon Kuri’ar zaben shugaban kasa da Atiku ya gabatar
Dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar da sakamakon kuri’un zaben shugaban kasa kamar yadda take a kwanfutan hukumar gudanar da zaben kasa (INEC).
A fadin sa “Hukumar INEC sun rage kuri’u na daga kwanfutan su ga sakamakon zaben jihohi 31 ta kasar da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu”
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Atiku Abubakar na barazanar cewa ya fiye shugaba Muhammadu Buhari da kuri’u ga zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairu. Dan takaran ya kuma gabatar da karar hakan a Kotun kara.
Atiku ya bayyana da cewa ya fiye Buhari da yawan kuri’u 1,615,302 ga zaben da aka gudanar a baya ta shekarar 2019.
“A yadda muka gano daga kwanfutan hukumar INEC, Sakamakon zaben shugaban kasa ta watan Fabrairun ya bayyana da cewa ina da kuri’u 18,356,732 fiye da Buhari da ke da kuri’u 16,741,430” inji Atiku Abubakar.
Kalli sakamakon da Atiku ya gabatar a kasa cikin karar da ya wallafa ga kotun kara ta birnin Abuja
______________________________________________________________________________________________________________________
Jiha Kuri’un da Atiku ya gabatar Kuri’u da INEC ta gabatar a baya
Adamawa 646,080 410,266
Akwa Ibom 587,431 395,832
Anambra 823, 668 524,738
Bayelsa 332, 618 197, 933
Benue 529,970 356, 817
Borno 281,897 71, 788
Cross River 572, 220 295, 737
Delta 778,369 594, 068
Ebonyi 565, 762 258, 573
Edo 677,937 275,691
Enugu 698,119 355,553
FCT 419,724 259,997
Gombe 684,077 138,484
Imo 485,627 334,923
Jigawa 539,522 289,895
Kaduna 961,143 649,612
Kano 522,889 391,593
Katsina 160,203.
Kebbi 493,341 154,282
Kogi 504,308 218,207
Kwara 353,173 138,184
Lagos 1,103,297 448,015
Nasarawa 344,421 283,847
Niger 576,308 218,052
Ogun 438,099 194,655
Ondo 451,779 275,901
Oyo 527,873 366,690
Sokoto 552,172 361,604
Taraba 442,380 374,743
Yobe 306,841 50,763
Zamfara 379,022 125,123
Ya kuma bayyana da cewa hukumar ta kara masa kuri’u a Jihar Osun da Jihar Filatu
A Jihar Osun, PDP sun gabatar da cewa suna da kuri’u 337,359 maimakon kuri’u 337,377 da hukumar INEC suka bayar.
A Jihar Filatu kuma PDP ta bayyana da cewa suna da kuri’u 273,031 maimakon 548,665 da hukumar INEC ta gabatar a sakamakon zaben.