Connect with us

Uncategorized

CP Wakili bai da damar kamun Gawuna da Sule – inji Ganduje

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Kano, CP Muhammed Wakili da rashin sanin daman sa da kuma nuna son wani bisa wani.

Ganduje ya bayyana hakan ne a wata ganawar sa da manema labaran BBC.

“Ba gane da shi ba kamin wannan lokacin, amma yadda yake tafiyar da aikin sa na bukatar bincike” inji Ganduje.

“Wakili ya gabatar da son Jam’iyyar guda bisa guda ga zaben da aka yi a Jihar Kano a baya. Wannan abin ya nuna da cewa bai san aikin sa ba, kuma ya bukaci bincike” inji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Kano, CP Wakili ya kame mataimakin gwamnan Jihar Kano da Sule Garo, akan zargin kadamar da makirci da tayar da hankali cikin dakin kidayar zabunan Jihar.

Ganduje ya kara da fadin cewa CP Wakili bai da daman kame Gawuna da Sule a yadda yayi a baya.

“Wannan ya bayyana da cewa Wakili bai san aikin sa ba a matsayin kwamishanan ‘yan sanda”

Ko da shike, a wata sanarwa jami’an tsaron ‘yan sandan sun bayyana da cewa ba wai sun kame mataimakin gwamnan bane, kawai ne sun yi kokarin kare shi daga farmaki da tanzoma da ya auku cikin dakin kirgan zabe a ranar.

Karanta wannan kuma: Makiyayan Jihar Benue sun kashe mutane 10 da bindiga a yayin da suke barci