Connect with us

Uncategorized

INEC ta gabatar da Yahaya Abdullahi mai nasara ga zaben Gidan Majalisar Jiha

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar kadamar da zaben kasar Najeriya (INEC) a ranar Alhamis da ta gabata sun gabatar da dakatar da sake zaben kujerar gidan majalisa a yankin Agaie kamar yadda aka sanar a baya.

Naija News Hausa ta gane a baya da cewa hukumar ta ki sanar da mai nasara ga zaben kujerar dan gidan majalisar wakilai ta yankin Agaie a zaben da aka yi a baya.

Hukumar INEC, a jagorancin Farfesa Sam Egwu, shugaban kadamar da hidimar zaben Jihar Neja ga zaben 2019 ya bayyana a ranar Alhamis a wata ganawa da cewa dan takaran kujerar gidan majalisar wakilai ta Jihar Neja daga yankin Agaie, a jam’iyyar PDP, Yahaya Abdullahi ne ya lashe zaben Gidan Majalisar.

Ya bayyana da cewa wannan matakin sanadiyar sakamakon da Malamin zaben yankin, Farfesa Musa Kolo ya gabatar ne, na cewar dan takaran daga jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben.

Egwu ya kara da cewa a halin yanzu an dakatar da sake zabe a yankuna biyu ta Jihar bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Ko da shike ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar, Mohammed Jibril ya nuna rashin amincewar shi da matakin da hukumar INEC ta dauka na gabatar da dan takaran jam’iyyar PDP ga kujerar dan gidan majalisar wakilan ta yankin Agaie.

“Me zai sa hukumar INEC ta dauki irin wannan matakin, bayan da yake a sane da cewa dan takaran mu ya fiye Abdullahi da kuri’u” inji Jibril.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar da cewa hukumar INEC sun rage yawar kuri’un da ya samu ga zaben 2019.