Uncategorized
Jihar Neja ta gabatar da kashin Biliyan N3.2b don gyara Gidan Gwmnati
A wata sanarwa ta yau, Jumma’a, 22 ga watan Maris, an sanar da cewa Gwamnatin Jihar Neja ta kadamar da kashe kudi kimanin naira Biliyan N3.2b don sake tsarafa ginin gidan gwamnatin Jihar da ke a Minna, babban birnin Jihar Neja.
A bayanin Zakari Jikantoro, Kwamishanan Aikace-aikacen Jihar Neja, ya bayyana ga manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata a garin Minna da cewa aikin gidan gwamnatin ya kasu biyu ne.
Jikantoro ya cigaba da cewa kashi na daya ya riga ya ci kudi naira biliyan N2.1 wanda aka riga aka gama da aikin; Kashi ta biyun kuma zai ci kimanin kudi naira biliyan N1.6, kuma an riga an bayar da aikin ga ma’aikata.
Ya kara da cewa kashi na biyun aikin ya kunshi gina gidan baki, wajen iyo ko ninkaya da sauransu.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Abubakar Sani Bello, Gwamnan Jihar Neja ya kafa wata kwamiti da za ta samar da mafita ga raguwa da kuma matsalar issashen karfin wutan lantarki da ake fuskanta a Jihar.
Gwamnan ya bayyana da cewa wutan tsawon awowi shidda (6Hrs) da hukumar Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ke bayar wa ga kananan hukumomin Jihar bai dace ba.
Karanta wannan kuma: Wata mugun tsawa ta kashe mutane 3 a karamar hukumar Ughelli ta Jihar Delta