Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 22 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 22 ga Watan Maris, 2019

1. Kotun Kara ta CCT na barazanar jarun manema labarai

Danladi Umar, Ciyaman na Kotun kara yayi barazanar cewa zasu jefa manema labarai a gidan jaru akan zargin cewa manema labarai basa yada gaskiya a rahoton su.

Umar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis da ta gabata, bayan da ya ci karo da wata zance a jarinda game da zaman kotun.

2. Hukumar INEC sun gabatar da ranar da zasu sanar da sakamakon zaben Jihar Rivers

Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya (INEC) ta gabatar da lokacin da zasu gabatar da rahoton sakamakon zaben gwamnoni ta Jihar Rivers.

Hukumar sun bayar da cewa zasu sanar da sakamakon zaben tsakanin ranar 2 zuwa 5 ga watan Afrilu a cikin shekarar 2019.

3. Hukumar Karban Harajin Kasa (FIRS) sun karyace zancen kara kudin Haraji

Mista Wahab Gbadamosi, Shugaba daga hukumar Harajin Kasa daga fanin Sadarwa ga hukumar ya bayar a wata sanarwa da cewa ba gaskiya bane zargi da jita-jitan da ya mamaye yanar gizo na cewar hukumar na da shirin kara kudin harajin kasa don cin ma biyar ma’aikatan kasa kankanin albashi na naira dubu talatin (30,000) da aka gabatar a baya.

Naija News Hausa ta sanar a baya a shafin Manyan Labarun Kasar Najeriya da cewa ana zargin Hukumar da kara harajin kasar Najeriya.

4. Karya ne, Ban dakatar da Tallafin kudin Masana’anta ba – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya shawarci ‘yan Najeriya duka da yin watsi da jita-jitan cewa Gwamnatin Tarayya a jagorancin Osinbajo ta dakatar da hidimar bada Tallafin kudi ga masu sana’a.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne daga bakin kakakin yada yawun shi, Mista Laolu Akande, a ranar Laraba da ta gabata a wata sanarwa da cewa bai dakatar da hidimar ‘Trader Moni’ ba.

5. Ba za a yi wata karin zabe ba a Jihar Adamawa Asabar ta gaba – inji Kotun Kara

Kotun kara tayi barazanar cewa ba za a gudanar da wata zabe ba a Jihar Adamawa ranar Asabar da gaba.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa hukumar gudanar da zaben kasa ta sanar da cewa zasu kadamar da zabe a Jihohin da aka samu matsalar zaben gwamnoni Jiha a baya, wanda hukumar ta gabatar da ranar 23 ga watan Maris don karshe zaben.

6. A bincike Sojojin Najeriya akan hidimar su ga zaben 2019 – Falana

Lauyan Yaki da Yancin Al’umma, Femi Falana (SAN), ya kalubalanci Gwamnatin Tarayya da yin bincike akan Sojojin Najeriya akan yadda suka kadamar da aikin su ga zaben shekarar 2019, musanman a Jihar Rivers da wasu Jihohin kasar.

“Shugaba Muhammadu Buhari da Hukumar INEC ba su samar da Sojojin ba don tsare rayuka ko hidimar zaben Jihar Rivers. Sojojin sun tafiyar da makirci ga aikin su” inji shi.

7. Okorocha yayi karar Hukumar INEC

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, yayi karar hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) da zargin cewa hukumar taki bashi takardan dama ta komawa kan kujerar Sanata.

Okorocha ya gabatar da karar ne a gaban Kotun Koli ta Abuja, babban birnin Tarayyar Kasa.

8. Tinubu yaki amince da Matan sa ga sabon matakin da ta dauka

Shugaban Jam’iyyar APC na Tarayyar kasar Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana rashin amincewa da sabon shirin matan sa, Sanata Oluremi Tinubu, akan neman kujerar mataimakiyar shugaban Sanata a Rukunin Sanata ta 9.

Naija News ta gane da hakan ne kamar yadda aka gabatar a wata sanarwa.

9. Jam’iyyar PDP ta kalubalanci Hukumar INEC akan zaben 2019

Jam’iyyar a zaman tattaunawa da suka yi na Kwamitin Manyan Shugabannan Tarayyar Kasa, sun gabatar da cewa Hukumar INEC ce sanadiyar matsalar da aka samu ga zaben kasar Najeriya a shekara ta 2019.

PDP ta bayyana hakan ne a wajen tattaunawar da aka yi a ranar Laraba, 20 ga watan Maris da ta gabata.

 

Ka samu cikakken labarun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausaa koyaushe.

Advertisement
close button