Connect with us

Uncategorized

An hari motar da ke dauke da kayan zabe a Jihar Benu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yayin da Malaman gudanar da zabe ke batun tafiya daga Ofishin hukumar INEC zuwa runfunar zaben su, don gudanar da ayukan su a matsayin malaman zabe a hidimar zaben Gwamnoni ta Jihar Benue a yau, 23 ga watan Maris kamar yadda hukumar ta gabatar a baya, ‘Yan Hari da makami da ba a gane da su ba sun fada wa motar da ke tafe da malaman zaben da hari.

An bayyana ga Naija News da cewa abin ya faru ne a hanyar Zaki Biam a nan karamar hukumar Ukum ta Jihar Benue, inda ‘yan harin suka bar wasu ma’aikata da mabiyan motar da raunuka da dama.

Abin ya faru ne a yayin da malaman zaben ke kokarin kai kayan zaben a runfar zabe da ke a yankin Azendeshi a nan Jihar.

Wani daga cikin jami’an tsaro da ke biye da motar, Daniel Pila ya bayar ga manema labarai a da yanayin a layin twitter na sa.

Ga sakon nan a kasa kamar yadda aka bayar a layin twitter;