Connect with us

Uncategorized

An sace Malaman zabe hudu a Jihar Bauchi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoto ta kai ga Naija News Hausa da cewa ‘yan hari da bindiga a Jihar Bauchi sun sace Malaman zabe hudu.

Wannan harin ya jawo tsauracewa tsakanin malaman zabe da masu jefa kuri’a a Jihar, a yayin da kowa na ta sai yaya ga hidimar zaben.

An bayyana da cewa abin ya faru ne a runfar zabe ta ’02’, mai lamba 010 da ke a karamar hukumar Jamare a Jihar.

A bayanin wani malamin zabe da aka kai a yankin da kuma ya samu tsira daga harin ‘yan ta’addan, ya bayar da cewa ‘yan harin sun sace malaman zaben ne da akwatin zabe da kayakin zabe duka.

Ya bayyana da cewa a yayin da abin ya faru, an kawo jami’an tsaro cikin motar Toyota Hilux bakwai a wajen da abin ya faru.