Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Kalli dalilin da ya sa Shugaba Buhari yayi watsi da neman zabe ga Gwamnonin APC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Asabar, 23 ga Watan Maris 2019 da ya gabata, Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta kadamar da hidimar zaben Gwamnoni da sauran zabanni da ba a samu karshe wa ba akan wasu matsaloli a Jihohin kasar. kamar yadda Naija News Hausa ta sanar a baya.

Bashir Ahmad, Mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari wajen samar da labaru a yanar gizo, ya gabatar a ranar Asabar da ta gabata da cewa jam’iyyar APC sun bukaci shugaba Buhari da ziyarar Jihohi don taimaka wa APC da yakin neman zabe ga masu takaran Gwamna a Jihohin da aka samu matsalar zabe a baya, amma sai shugaba Buhari yayi watsi da ziyarar, kusan ‘yan lokaci kadan da yake shirin yin hakan.

A wata bayyanin ta ranar 23 ga watan Maris 2019 da ta gabata, Ahmad ya gabatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da ziyarar ne da fadin cewa ya kamata a bar mutane su zabi duk dan takaran da suke bukata da kuma so, amma ba wai don shi ba.

“A bar mutane su zabi dan takaran da suke bukata da jagorancin su, amma bai wai suyi zabe ba don ni” inji shugaba Buhari, a fadin Bashir.

Kalli sakon a kasa daga layin Twitter;

Ko da shike Naija News Hausa a wata sanarwan Manyan Labaran Najeriya ta yau, mun sanar da cewa Hukumar INEC ta gabatar da dan takaran kujerar gwamna ta Kano daga jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, a matsayin mai nasara ga zaben ranar Asabar da aka gudanar.

Kamar yadda INEC ta gabatar, Ganduje ya lashe zaben ne da yawar kuri’u 1,033,695 fiye da dan adawan sa daga Jam’iyyar PDP.

Karanta wannan kuma: ‘Yan Hari sun kashe Dan Sanda guda da kuma sace biyar a Jihar Zamfara