Connect with us

Uncategorized

Gobarar wuta ya kame wani Makarantar Sakandiri a Jihar Kano

Published

on

Naija News Hausa ta samu sabuwar rahoto da cewa gobarar wuta ya kame aji bakwai (7) a makarantan Sakandirin Badawa ta Jihar Kano a yau Litini, 25 ga watan Maris 2019.

An gabatar ne da cewa makarantar ta kame da wuta ne a missalin karfe 1:30 na safiyar ranar Litini (yau), ‘yan awowi kadan da ‘yan makaranta da mallaman su ke shirin zuwa makarantar don kadamar da ayukan karatu kamar yadda aka saba.

DSP Abdullahi Haruna, Mai yada labarai ga Jami’a tsaron yankin ya bada tabbacin lamarin a wata sanarwa da yayi a yau da cewa lallai Aji bakwai ne suka kone a gobarar wutan a missalin karfe 1:30 na safiyar yau Litini.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa

DSP Haruna ya bayar da cewa gobarar ya faru ne sakamakon gamewar wayar wutan lantarki a daya daga cikin ajin da ke makarantar.

“Ko da shike babu wanda ya mutu ko samu rauni sakamakon gobarar, amma ajujuwa bakwai suka kone. Daga baya kuma Hukumar Kashe Gobarar wuta suka isa wajen don kashe yaduwar wutan” inji shi.