Kalli yadda wayar Salula ta kusan hallaka rayuwar wani matashi

Wani matashi ya gabatar da yadda wayar Salula ta SAMSUNG ta tashi hallaka shi

Wani Matashi mai amfani da wayar salula ta SAMSUNG ya bayyana mugun abin da ya tashi faruwa da shi a yayin da wayar sa ta fashe kamar Bam.

Kamar yadda matashin ya bayyana a shafin yanar gizon nishadarwa ta twitter, Naija News Hausa ta iya gane da cewa wayar ta kame ne da wuta kamar tashin Bam a aljihun matashin.

Matashin da ke da likin suna ta twitter; @of_pablosoares ya bayyana ne da cewa wayar ta kame ne da wuta ba tare ya hada ta da wutar lantarki ba ko da wata na’ura.

“Alo, Ku kalla, Wayar salula ta mai lamba ‘S7edge’ da layi biyu cikin ta ya kame da wuta ba tare da na hada ta da wata wutar lantarki ko na’ura ba”

“yaya kenan zai zama da ace wayar na ga aljihun gaba na kamin abin ya faru? ai da watakila wayar ta hallakar da ni” inji shi.

“Sai da na jefar da wayar cikin bokitin ruwa kamin na iya dakatar da kamun wutar. A ganewa na, ya kamata mu dinga kula da yadda muke barin kananan yara ke kusantar wayar salula da kuma la’akari da yadda muke amfani da ita a koyaushe” inji Saurayin.

 

Karanta wannan kuma: Kalli yadda masoyan Ali Nuhu suka taya shi murnan ranar haifuwa