Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Karanta Takaitaccen Labarin Sani Danja

Published

on

Ga Takaitaccen labarin Shahararran dan shirin wasan fim na Kannywood, Sani Danja

Sani Danja, kamar yadda aka fi sanin sa da suna, daya ne daga cikin shaharrarun ‘yan shirin fim ba Kannywood da ake ji da su.

Ainihin sunansa Danja ita ce; Sani Musa Abdullahi, ko kuma Sani Musa Danja.

An haifi Sani Danja ne a ranar 20 ga watan Afrilu ta shekarar 1973 a nan garin Fagge, ta Jihar Kano, a kasar Najeriya. Bincike ya bayyana da cewa Sani Musa Abdullahi ya samu likin Danja ne a lokacin da yake karami, dalilin suna kuwa itace irin halin da Sani ke da shi na rashin ji a lokacin. Kawai abokanan wasa suka laka masa sunan ‘Danja’ wanda a yau ko ina ka kira Sani Danja an riga an gane ko da wa kake.

Alhaji Musa Abdullahi, Baban Sani Danja na da diya bakwai ne. Maza biyar da Mata biyu. Sunan Maman Danja kuma ita ce, Hajiya Risikat.

Sani Danja kuma na da Aure da Mansura Isah tun shekarar 2007.

Karanta wannan kuma: Ba na son Auren mai Kudi – inji Jaruma Jamila Nagudu

Tarihin Karatun Sani Danja

Sani Danja ya fara karatun sa na farko ne a Makarantar Firamare da ake ce da ita `Yan Sanda Special Primary School, anan Jihar Kano daga shekarar 1979 zuwa shekarar 1980, bai karshe karatun Firamaren sa a nan ba sai da ya kara gaba zuwa ‘Kano Capital Primary School’, inda ya fara daga farko kuma daga shekarar 1980 zuwa 1985.

Bayan hakan, Danja ya shiga karatun Sakandiri ta farko a ‘Government Junior Secondary School Kawaji’ inda yayi karatun sa na shekaru ukku, daga shekarar 1985 zuwa 1989, kamin dada ya kara gaba zuwa Babban Makarantar Sakandari ta Rumfa, ya kuma kamala shekarar sa ukku anan, daga shekarar 1989 zuwa 1991.

Danja yayi karaun sa ta Jami’ar farko ne a Makarantar Jami’a ta Kano inda ya karbi takardan karutun sa ta NCE a nan ‘FCE Kano’ a shekarar 2004.

Sani Danja ya fara tashen rawa da raye-raye ne tun yana dan shekara 12. Abokansa da ‘yan anguwa kuma kan yaba masa kwarai da gaske tun lokacin, saboda irin murya da kuma taken rawa da yake da ita.

Danja na daya daga cikin wata kungiyar rawa da ake ce da ita YKK a lokacin, kamin dada a baya suka rabu akan wata dalili. daga nan kuma Danja ya shiga shirin nasa waka shi kadai. Wakan sa ta farko a lokacin ita ce `Yaki-taho-yaki’.

Shirin Fim

Sani Danja ya shiga shirin fim na Hausa ne a shekarar 1999. Ya kuma samu fita a shirin sa na farko da aka sanya wa liki `Students’, a Hausance ‘Dalibai’. 

Daga wannan shirin sai Danja ya zama jigo a kamfanin shirin fim na Hausa, ya kuma fito daga fim kamar `Adon kishiya’ a shekarar 2000, `Kwarya tabi Kwarya’ dadai sauran su.

Ga Shirye-Shirye da Sani Danja ya samu fita a Kannywood;

 • ‘Yan Uwa
 • ‘Yar Agadez
 • A Cuci Maza
 • Adali
 • Albashi (The Salary)
 • Nijeriya Da Nijar
 • Sa’ah
 • Sabon Shafi
 • Sai Na Dawo
 • Sameeha
 • Sani Nake So
 • Shelah
 • So Sanadi
 • The Other Side
 • Ango Da Amarya
 • Ban Ga Masoyi Ba
 • Bani Adam
 • Binta Suga
 • Fitattu
 • Gani Gaka
 • Gabar Cikin Gida
 • Gambiza
 • Garin Dadi
 • Gurnani
 • Gwanaye
 • Ijaabaah
 • Kukan Zaki (the Lion’s Cry)
 • Makauniya
 • Matakin Aure
 • Mijina Sani
 • Na’imatu
 • Nageria
 • Ummi
 • Wata Shariar
 • Wata Tafi Wata
 • Ya Humaira
 • Yammaci
 • Zazzabi
 • Buri Uku A Duniya (My Three Wish in the world), Da dai Sauran su.