Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 25 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 25 ga Watan Maris, 2019

1. Hukumar EFCC ta gabatar da neman kamun Ayodele Oke da Matansa

Hukumar Bincike da Yaki akan Cin Hanci da Rashawa da Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta gabatar da bukatan kame Darakta Janar na Hukumar (NIA), Ayodele Oke, da matan sa Folashade, akan zargin wata halin cin hanci da rashawa da aka gane su da ita.

Mista Tony Orilade, Mai yada labarai ga hukumar EFCC ne ya gabatar da wannan a wata sanarwa ta ranar Lahadi da ta gabata.

2. PDP: Samuel Ortom ya lashe zaben kujerar Gwamna ta Jihar Benue

Hukumar kadamar da hidimar zaben kasa, INEC ta gabatar da dan takaran kujerar Gwamna ga tseren zaben 2019 daga jam’iyyar PDP, Samuel Ortom a matsayin mai nasara ga zaben kujerar Gwamnan Jihar.

Hukumar ta gabatar da hakan ne bayan da aka kamala zaben ranar Asabar da ta gabata a Jihar.

3. Jam’iyyar YPP ta Jihar Bayelsa sun zargi INEC da ware su daga takaran zabe

Jam’iyyar YPP daga Jihar Bayelsa sun kalubalanci Hukumar INEC da zargin cewa hukumar ta tsige Jam’iyyar su daga takardan zabe ga zaben da aka yi ta ranar Asabar da ta gabata.

Jam’iyyar sun gabatar ne da hakan daga bakin Sakataren yada labarai ga Jam’iyyar, Egbeola Martins.

4. Dalilin da ya sa na janye daga Jam’iyyar PDP – Gbenga Daniel

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Mista Gbenga Daniel, yayi watsi da jita-jitan cewa ya janye ne daga Jam’iyyar PDP akan wata yarjejeniya da yayi da jam’iyyar APC.

Mista Daniel ya karyace wannan zancen da cewa ba gaskiya bace. kamar yada muke da sani a Naija News Hausa da cewa Mista Gbenga Daniel ya gabatar ne da janye daga jam’iyyar PDP ‘yan makonnai da suka shige a wannan watan.

5. Bala Mohammed daga PDP ya lashe zaben Jihar Bauchi

An gabatar da Bala Mohammed, dan takaran kujerar gwamna daga Jam’iyyar PDP a matsayin mai nasara ga lashe tseren zaben Gwamnan Jihar Bauchi.

Hukumar INEC ta gabatar ne da nasarar Bala daga bakin babban Malamin zabe da ke jagorancin zaben Jihar, Farfesa Kyari Mohammed a ranar Lahadi 24 ga watan Maris da ta wuce.

6. PDP: Tambuwal ya sake lashe kujerar Gwamnan Jihar Sokoto

Dan takaran kujerar Gwamna daga jam’iyyar PDP ta Jihar Sokoto, Gwamna Aminu Tambuwal ya sake lashe zaben gwamnan Jihar Sokoto ga zaben da aka gudanar a Jihar ranar Asabar, 23 ga watan Maris 2019 da ta gabata.

Naija News ta gane da cewa Tambuwal ya lashe zaben ne da yawar kuri’u 512,002 fiye da dan takaran kujerar Gwamnan Jihar daga Jam’iyyar APC, Ahmad Aliyu da ke da kuri’u 511,661.

7. APC: Simon Lalong ya lashe zaben Jihar Filatu

Dan takaran Kujerar Gwamnan Jihar Filatu daga Jam’iyyar APC, Simon Lalong, ya sake lashe tseren zaben kujerar gwamnan Jihar ga zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta wuce.

Bayan zaben, Naija News ta gane da cewa Lalong ya lashe tseren takaran ne da kuri’u 583,255 fiye da dan takaran Jam’iyyar PDP da ke da yawar kuri’u 538,326.

8. Dalilin da ya sa Buhari bai taya ‘yan takaran APC da yakin neman zabe ba – Shugabancin kasa

Mai Taya shugaba Muhammadu Buhari ga yada labarai a yanar gizo, Bashir Ahmad, ya gabatar da dalilin da ya sa shugaban bai ziyarci Jihohin kasar ba don taya ‘yan takaran kujerar Gwamna daga Jam’iyyar APC da yakin neman zabe ba.

Naija News Hausa ta gane da cewa shugaba Buhari bai kara yawon yakin neman zabe ba, tun bayan da aka gabatar da shi mai nasara ga zaben shugaban kasar Najeriya ta karo na biyu.

9. Hukumar INEC ta gabatar da Ganduje mai nasara ga zaben Jihar Kano

Hukumar gudanar da zaben Kasa (INEC) ta gabatar da dan takaran kujerar gwamna daga jam’iyyar APC, Gwamna Umar Ganduje a matsayin mai nasara ga zaben Jihar Kano.

Naija News Hausa ta gane da cewa Ganduje ya lashe zaben ne da fiye dan adawan sa da yawar kuri’u 9,000 bayan da hukumar INEC ta kamala kirgan zabe.

Ka samu cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa