Uncategorized
Kotu ta bayar da dama ga Hukumar INEC don kamala zaben Jihar Adamawa
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kotun Koli ta hana Hukumar INEC da ci gaba da hidimar zaben Jihar Adamawa akan wata kara da Kotun ke yi ga zaben Jihar.
A yau Talata, 26 ga watan Maris 2019, Alkali Abdulaziz Waziri daga Kotun Koli ta Jihar Yola, babban birnin Jihar Adamawa, ya gabatar da bada dama ga Hukumar INEC don ci gaba da kadamar da hidimar zaben Jihar.
Mun gane a Naija News Hausa da cewa kotun daman ta dakatar ne da hukumar ga gudanar da zaben Jihar akan wata karar da dan takaran kujerar gwamnan Jihar daga Jam’iyyar (MRDD), Mustafa Shaba, ya gabatar ga kotun kwanakin baya da suka shige.
Mustafa Shaba yayi karar ne daman da zargin cewa hukumar INEC ta cire tambarin jam’iyyar daga cikin takardan zaben gwamnoni da aka yi a ranar 9 ga watan Maris da ta gabata a kasar.
A yau Talata, Alkalin, Malam Waziri ya gabatar da janye karar. ya kuma bayar da dama ga hukumar da ci gaba da hidimar su.
Ko da shike kotun ta bayyana da cewa zata karshe duk wata bayani game da karan a ranar 27 ga watan Maris, watau Laraba ta gaba.
Bisa zaben da aka yi a baya a Jihar, Sakamakon zaben ya bayar da cewa dan takaran gwamnan Jihar daga jam’iyyar PDP, Hammadu Fintiri, na gaba da yawar kuri’u 367,471, shi kuma Jubrilla Bindow, dan takaran kujerar gwamna daga jam’iyyar APC na da kuri’u 334,995.