Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari sun sace wani Firist na Katolika a Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu Mahara da Makami sun sace wani Firist na Ikklisiyar Katolika da ke a Jihar Kaduna.

Kamar yadda Naija News Hausa ta samu rahoton lamarin a wata sanarwa daga bakin kakakin yada yawun jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar, Mista Yakubu Sabo. Ya bayyana da cewa abin ya faru ne ranar Litinin da ta gabata, inda ‘yan harin suka saci Firist din a wata kauye ake ce da ita Ankuwa, a karamar hukumar Kachia.

Mista Sabo ya bayyana da cewa abin ya faru ne a missalin karfe 8:00 na daren ranar Litini a yayin da Firist din ke zaman sa a gida.

“An sace Firist din ne da gaske, kuma ba wanda ya san inda aka tafi da shi” inji Sabo.

“A halin yanzu, an watsar da darukan tsaro don zagaye anguwar da binciken yankunan ko za a gane inda ‘yan harin suka tafi da Firist din, a kuma yi kokarin ribato ran sa” inji bayanin Mista Sabo.

Ya kuma bukaci mutane da bayar da duk wata alama da suka gane da ita game da yadda za a samu ribato Firist din.

Karanta wannan kuma: Ku mayar mana da Shanayan Mu – Fulani sun gaya wa ‘Yan Sandan Jihar Kaduna