Connect with us

Uncategorized

INEC ta baiwa ‘yan Gidan Majalisa Takardan shugabanci a Jihar Kebbi

Published

on

at

advertisement

Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa ta Jihar Kebbi ta bayar da takardan komawa ga kujerar wakilci ga ‘yan Majalisar Wakilan Jihar.

Hukumar tayi hakan ne a jagorancin babban Malamin zaben Jihar, Alhaji Muhammad Mahamud, a ranar Talata da gabata a nan Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

Mahamud, a yayin da yake bayar da takardan ga ‘yan gidan Majalisar guda 25, ya shawarce su da tabbatar da cewa sun kadamar da ayukan su yadda ya kamata a Jihar.

“Ku tabbatar da cewa a matsayin ku na ‘yan gidan Majalisar Wakilai, kun kadamar da ayukan da ya kamata, ku kuma wakilci mutanen da suka zabe ku a Jihar ku duka” inji shi.

Biyu daga cikin ‘yan Majalisar; Alhaji Isa Rukubalo da ke wakilcin yankin Yauri, da kuma Alhaji Samaila Bui da ke wakilcin yankin Arewa, sun buga gaba da cewa lallai zasu kadamar da aikin su yadda ya kamata a yankunan su duka.

Karanta wannan kuma: Ga cikakken kuri’un zaben Gwamnonin Najeriya ta Jam’iyyar APC da PDP ga zaben 2019