Connect with us

Uncategorized

Sheikh Ahmad ya samu Tsira daga hannun ‘yan hari

 

‘Yan Hari da makami sun saki Sheikh Ahmad Sulaiman, Malamin Arabi da aka sace a Jihar Katsina, kwanakin baya.

Mun sanar a kwanakin baya a Naija News Hausa da cewa ‘yan hari da makami sun sace Sheikh Ahmad Sulaiman, Masoyin Shugaba Muhammadu Buhari.

Malam Muhammad Kabir, daya daga cikin iyalan malamin ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wata ganawa.
Ya ce “Sheikh na cikin koshin lafiya, ba wata matsala da shi”

“Sheikh Sulaiman na kan hanyar zuwa Kano a yadda nike baku wannan bayanin, ina tabbatar maku da cewa lallai ‘yan hari da makamin sun sake shi. Muna kuma nuna godiya ga Allah don yadda ya kare rayuwar Sheikh daga hannun ‘yan ta’addan” inji Kabir.

Naija News Hausa ta gane da cewa ‘yan harin sun sace Sheikh Sulaiman ne hade da wasu Malaman Arabi biyar a yayin da suke kan tafiya a hanyar Sheme da ta bi Kankara, a Jihar Katsina ‘yan kwanaki goma sha ukku da suka gabata.

Tafiyar tasu ta bi ne daga Jihar Kebbi zuwa Jihar Kano kamin dada suka ci karo da ‘yan hari da makami a kan hanya.

Ko da shike, a halin yanzu ba a bayyana ba ko an saki sauran malaman da ke tare da shi, amma akwai tabbaci da cewa an saki Sheikh Ahmad.

Mun kuma sanar a shafin labaran mu a baya da cewa ‘yan hari sun bukaci a biya su kudi kimanin naira Miliyan N300m kamin su saki malamin.

A halin yanzu ba tabbacin cewa ko wata kila an biya kudin kamin ‘yan harin suka saki malamin. Amma zamu sanar a shafin labaran mu idan wata bayani game da hakan da ta biyo a baya.

Advertisement
close button