Connect with us

Uncategorized

Tau ga wata: Maganin Bindiga ya karye a yayin da wani ya rasa ransa garin gwada karfin magani

Published

on

Abubakar Hamisu, wani mai shekaru 40 a Jihar Katsina ya mutu sakamakon gwada karfin maganin bindiga.

Kamar yadda aka bayar bisa labari, abin ya faru ne a ranar 16 ga watan Maris ta shekarar 2019 a karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

An bayyana ne da cewa Hamisu da abokannan sa na gwajin karfin wata maganin bindiga ne da suka samu, a yayin gwajin ne aka harbi Abubakar Hamisu har ga mutuwa.

Bincike ta nuna da cewa Rabe Salisu, abokin Hamisu, shi ma ya samu raunukan harsasun bindiga a yayin da suke gwada kyan maganin da harsasu.

Hamisu da Salisu na daga kauyen Kwari ne a karamar hukumar Jibia, Jihar Katsina.

‘Yan Sandan yankin sun gabatar da cewa an kame Mani Mohammed, mutumin da ya harbe Hamisu. Ko da shike an bayyana da cewa a fadin sa, ba wai ya so hakan bane, da cewa bindigar ta tashi ne a yayin da yake kokarin anshe bindigar daga hannun Hamisu da Salisu a lokacin da suke kokarin gwada maganin bindigar a jikin su.

Mohammed na da shekaru 43, kuma aboki ne da kuma mazaunin kauye guda da Hamisu da ya mutu da kuma Salisu abokin su da ya samu raunukar bindiga.

“Bindigar ta tashi ne a yayin da nike kokarin karban bindigar daga hanun Marigayi Hamisu da kuma hannun Salisu”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wata Macc a Jihar Bauchi, ta tsage cikin ta da reza don zafin na’uda

Ko da shike an kai Hamisu da Salisu a Asibitin Janara ta Jibia, amma abin takaici, Hamisu ya mutu a yayin da ake basu kulawa.

A halin yanzu, an bayar da cewa an riga anyi karar Mani a gaban Babban Kotun kara ta Jihar Katsina a ranar Talata da ta gabata don kadamar da kisan kai.

Alkalin da ke karar, Hajiya Fadila Dikko, ta daga karar zuwa ranar 7 ga watan Mayu ta shekarar 2019, sa’anan a ci gaba da karar daga inda aka tsaya.

Ofisan Jami’an ‘Yan Sanda da ke jagorancin karar, Sajan Lawal Bello, ya bayyana ga kotu da cewa zasu ci gaba da bincike akan karar.