Wani Matashi ya kashe dan Uwansa don kishi

‘Yan Sandan Jihar Jigawa sun kame wani matashi mai shekaru 22 da laifin kisan kai

An kame Gambo Sa’idu ne a kauyan Badakoshi da ke a karamar hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa, da zargin kashe dan ‘uwan sa akan wata gardama da ya tashi tsakanin su game da tumakin da suke kiwo shi da dan ‘uwan na sa.

Naija News Hausa ta samu gane wa kamar yadda Kakakin yada yawun ‘yan sandan yankin, SP Audu Jinjiri ya bayar ga manema labarai a Dutse, da cewa lallai Gambo ya kashe dan uwan sa ne Haladu mai shekaru 40 da Adda.

A bayanin jami’in, Ya ce hukumar su da ke karamar hukumar Gwaram ta karbi kirar gaugawa ne missalin karfe biyu na daren ranar Laraba, 27 ga watan Maris da ya gabata da cewa Gambo ya aiwatar da kisan kai.

SP Jinjiri ya kara da cewa darukan tsaro sun ziyarci inda abin ya faru kuma sun samu tabbacin al’amarin.

“Gambo ya hari dan uwan sa ne cikin daji a yayin da suke kiwo. Daga nan kuma ya kashe shi”
“Don kara bada tabbacin mutuwar Haladu, wani Dakta da ke yankin ya bincike shi ya kuma bada tabbacin cewa lallai ya mutu” inji Jinjiri.

SP Jinjiri ya gabatar da cewa bisa bincike, sun iya gane da cewa Gambo ya kashe dan uwan sa ne da kishin cewa Haladu ya fi shi yawar tarin tumaki.

Ana kuma zargin Gambo da shan mugun kwayoyi kamin ya aiwatar da kisan dan uwansa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa  wani ya kashe abokin sa a yayin da suke gwada karfin maganin bindiga