Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Jihar Jigawa ya kafa Kwamitin samar da Albashin Ma’aikata

 

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, Gwamnan Jihar Jigawa, ya nada wata sabuwar kwamiti na samar bincike ga biyar kankanin albashin ma’aikatan Jihar.

Gwamnan ya kafa kwamitin rukunin mutane goma sha biyar ne a ganewar Naija News don samar da yadda Jihar zata samu biyar kankanin albashin ma’aikata a sauwake.

Mun ruwaito a gidan labarun mu a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sanya Kwamitin bincike kan biyan kankanin albashin ma’aikatan kasa ta naira dubu talatin.

Naija News Hausa ta gane da matakin Gwamna Badaru ne a yayin da mataimaki ta musanman ga Gwamnan wajen yada labarai, Auwal D. Sankara, ya bayyana ga manema labarai a ranar Alhamis (yau) 28 ga watan Maris 2019.

Sankara ya ci gaba da bayyana da cewa Gwamnan ya sanya tsohon gwamnan Jihar, Ibrahim Hassan Hadejia, a matsayin shugaban kwamitin. Ya kuma sanya Hussaini Ali Kila a matsayin sakataren kwamitin.

Wannan matakin Gwamna Badaru ya biyo baya ne ganin sanya hannu da shugaba Muhammadu Buhari da Gidan Majalisar Dattijai suka yi ga dokar biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu 30,000.

Continue Reading
Advertisement
Advertisement
close button