Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 28 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 28 ga Watan Maris, 2019

1. Orji Uzor Kalu ya gabatar da shirin takaran Mataimakin Shugaban Gidan Majalisar Dattijai

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, da ya ci kujerar Sanata da ke wakilcin Arewacin Jihar Abia, ya gabatar da shirin takaran mataimakin shugaban gidan Majalisar Dattijai.

Kalu ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayar da bayani ga manema labarai a Filin Jirgin Sama ta Murtala Muhammed da ke a Jihar Legas, ranar Laraba da ta gabata.

2. Kotu Kara ta bada dama ga Atiku don kalubalantar Buhari

Kotun Kara da ke jagorancin karar zaben shugaban kasa ta bayar da dama ga Atiku da Jam’iyyar PDP don gabatar da karar su akan hidimar zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da aka gabatar da Buhari mai nasarar zaben.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, ya gabatar da cewa bai amince da sakamakon zaben 2019 ba.

3. APC ta Adamawa sun bayyana dalilin rashin amince da ranar zabe da INEC ta bayar

Jam’iyyar APC ta Jihar Adamawa sun bayyana da cewa basu amince da sabon ranar kadamar da hidimar zaben Jihar kamar yadda hukumar INEC ta gabatar a baya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Hukumar INEC ta bayar da ranar 28 ga watan Maris 2019 ga Jihar Adamawa don kamala hidimar zaben Jihar.

4. Lauyoyin Jihar Kano fiye da 100 sun shirya hakon Ganduje a Kotun Kara

Kimanin Lauyoyi 100 sun bayar da kansu don taimaka wa dan takaran kujerar Gwamna na Jam’iyyar PDP a Kano, Engr Abba Kabir Yusuf, don kalubalantar nasarar Abdullahi Umar Ganduje a Kotu, game da nasarar zaben Gwamnan Jihar.

An gabatar ne da hakan daga bakin Sanata Herssern Umar, Ciyaman na Kwankwasiyya.

5. Rahoto ya bayyana ‘yan Sandan Najeriya da halin Cin Hanci da Rashawa

Bisa bincike da Tarihi, wata Rahoto na Hukumar (SERAP), ya bayyana da cewa ‘Yan Sandan Najeriya sun fiye kowace rukunin da hukumomi a kasar da halin cin hanci da rashawa.

An kai ga wannan tabbaci ne bayan bincike da aka yi a Yankuna Shidda ta kasar Najeriya, hade ma da Abuja, babban birnin Tarayya.

6. Ana wata ga wata: Wani dan takaran shugaban kasa ya gabatar da wata Kara akan shugaba Buhari

Dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDM, Pastor Aminchi Habu, da Jam’iyyar sa sun gabatar da sabuwar kara akan shugaba Muhammadu Buhari, Hukumar INEC da kuma Jam’iyyar APC game da hidimar zaben 2019.

A cikin karar, dan takaran shugaban kasar, Pastor Habu ya bukaci kotun kara da yin watsi da gabatar da Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya.

7. Karya ce kuri’un da Buhari ya samu ga zaben 2019 – inji Buba Galadima

Buba Galadima, Kakakin yada yawu ga lamarin yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubaka, dan takaran shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, ya kara bayyana da cewa kuri’un da hukumar INEC ta gabatar na shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019 ba gaskiya bac ce inji shi.

Galadima ya fadi hakan ne don goyon bayan zargi da barazanar da Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) ke yi na cewar sun fiye Jam’iyyar APC da kuri’u ga zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar nan ga zaben 2019.

8. IGP Adamu ya gabatar da Matsalar da ‘Yan Sanda ke fuskanta ga gudanar da tsaro a kasar

Babban Shugaban Jami’an ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya gabatar da cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya na fuskantar matsalan isasshen kudi wajen kadamar da ayukan su.

Naija News Hausa ta gane da cewa Adamu ya gabatar ne da hakan a wajen zaman kwamitin hukumomin akan kasafin shekarar 2019.

9. Shugaba Buhari ya gabatar na zabin sa ga shugaban gidan Majalisar Dattijai

Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamnonin Jam’iyyar APC da Manyan shugabannin Jam’iyyar sun gabatar da zabin su ga Sanata Ahmad Lawan ga kujerar shugabancin gidan majalisar Dattijai.

Naija News Hausa ta gabe da cewa wannan matakin ya biyo ne bayan da Sanata Bukola Saraki ya fadi ga zaben kujerar Sanata daga Jihar Kwara.

10. Shugabancin Gidan Majalisar Dattijai ba ta kowace Jam’iyyar ba ce – PDP ta gayawa APC

Jam’iyyar PDP sun gabatar da cewa lallai Sanatocin Jam’iyyar PDP na da daman takaran kujerar shugabancin Gidan Majalisar Dattijai.

Jam’iyyar sun gabatar ne da hakan a wata sanarwa da aka bayar da kuma Kakakin yada yawun Jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan ya bayar ranar Talata da ta gabata.

Ka samu karin bayanin labarun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa