Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli abin da Kungiyar CAN suka gayawa Shugaba Muhammadu Buhari a yau

Published

on

Mun ruwaito ‘yan lokatai da suka shige da cewa Shugaba Muhammadu Buhari na zaman tattaunawa da Kungiyar  Addinin Kirista (CAN) a birnin Abuja a yau Jumma’a 29 ga watan Maris 2019.

‘Yan Kungiyar, hade da shugaban kungiyar, Reverend Samson Ayokunle da kimanin mambobi 30 sun halarci zaman tattaunawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa.

Mista Ayokunle ya fara da gabatar da cewa daya daga cikin muhinman ziyarar su itace don taya shugaba Buhari murna ga nasarar da ya samu ga tseren zaben 2019.

“Addu’ar mu itace, Allah ya kara maka duk wata Fasaha da kuzari yadda zaka iya karshe shugabancin ka ta karo biyu da kyau, fiye da yadda aka yi a shekaru hudu da suka gabata. Mun yi rokon Allah ya ba shugabancin ka karfin jagorancin kasar Najeriya da kyau zar ga cin nasara a kowace fanni, a cikin sunan Yesu Kiristi. Amin”

“Ina son ka gane da cewa wannan kungiyar na muradi da kuma yiwa shugabancin ka fatan nasara da alkhairi wajen taya ku da addu’a a koyaushe kamar yadda Littafi Mai Tsarki ta koya mana” inji Samson.

Mista Samson ya ci gaba da bayyana bukatun Kungiyar ga shugaba Muhammadu Buhari. Kalli bukatun a kasa kamar haka;

1. Kada ka bar Shugabancin ka ya kasance ga Jam’iyya kawai

Mista Samson ya ce ”Munyi murna kwarai da gaske ga jin bayanin ka bayan da hukumar INEC ta gabatar da kai mai nasara ga zaben, da cewar zaka tafiyar da shugabancin ka ne ga ‘yan Najeriya duka.

“Ina son kan rike wannan, ka kuma ga kanka a matsayin Uba ga ‘yan Najeriya duka”

2. Ka Magance Matsalar Addini ga samar da shugabannan gidan Majalisar Dattijai

Kungiyar mu na shawartan ka da kullawa da kuma tabbatar da cewa anyi adalci wajen sanyan shugabanai a gidan Majalisar Dattijai ba tare da nuna banbancin Addini ba.

3. Ka yi kokarin ganin cewa an ribato ran Leah Sharibu

Muna mai kuka da kira gareku ya shugaba Buhari, da yin anfani da duk wata dama da kake da ita wajen ganin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun saki Leah Sharibu da sauran ‘yan Makarantan Chibok da Boko Haram suka sace a baya.

“Kowace rana, iyayan yarannan da masoya na kasance da bakin ciki, musanman idan sun tuna da cewa yaran su da a kangin ‘yan ta’adda”

“Yin wannan zai karfafa amincin ka ga bayyanar ‘yan Najeriya duka. Zai kuma zama abin murna garemu duka da ganin cewa ba a yi watsi da ran yaran nan ba”

4. A karfafa Jami’an tsaro

Ya shugaba, mun jinjina wa gwamnatin tarayya d kuma jami’an tsaron kasar ga gwagwarmaya akan hidimar tsaron kasar nan. Amma muna kira da gareka da kara karfafa hukumomin tsaron kasar da ganin cewa sun kara karfi a hanyar samar da tsaro a kasar. musanman jihohin da ake samun matsalar tsaro a halin yanzu.

Kungiyar CAN ta gabatar da bukatar su da dama da kuma addu’a ga Allah da cewa shugabancin shugaba Muhammadu Buhari a wannan karo ta biyu zai zama da nasara fiye da ta da.