Connect with us

Uncategorized

Karya ne, ba mu daukan Ma’aikata a wannan lokacin – inji NIS

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Shiga da Fitan kasar Najeriya (NIS) ta gabatar da cewa basu daukar ma’aikata a halin yanzu.

Naija News Hausa ta gane da cewa Hukumar ta gabatar ne da hakan don mayar da martani ga jita-jita da halin magudi da ya mamaye yanar gizo da cewa hukumar na daukar ma’aikata.

Hukumar ta karyace zancen ne a wata sanarwa da aka bayar daga hannun Kwanturola Janar na Hukumar, Msta Muhammad Babandede, a birnin Abuja, ranar Alhamis da ta gabata.

Mista Sunday James, Ofisan yada labarai ga hukumar, ya rattaba hanu ga takardan don bada tabbacin hakan.

Shugaban hukumar, Muhammad Babandede, ya gane da wata layin yanar gizo, watau wannan; www.nisrecruitment.com.ng wanda wasu ke amfani da ita don karban kudi daga hannun mutane da sunan cewa hukumar NIS na daukar ma’aikata.

A wannan layin yanar gizon ta saman, an riga an cuci yawancin mutane da jan ra’ayin su da biyan wasu kudade don cika fom na NIS.

Karanta wannan kuma: ‘Yan Hari da makami sun saki Sheikh Ahmad Sulaiman, Malamin Arabi da aka sace a Jihar Katsina, kwanakin baya.

“Ina fadi ga fili ga al’ummar kasar Najeriya gaba daya da cewa hukumar mu bata daukar ma’aikata a halin yanzu”

“Kada ku yadda a yaudare ku a wannan layin www.nisrecruitment.com.ng ko wata. duk karya ce, kuma hanyar karban kudin ku kawai suke kadamar wa“ inji Babandede.

“Duk wata hidimar daukan ma’aikata a hukumar mu, zamu gabatar da shi a layin yanar gizon hukumar mu ta ainihi. Watau www.immigration.gov.ng” inji shi a yadda ya bayar ga kungiyar manema labaran kasar Najeriya.