Connect with us

Uncategorized

Kotu ta saka wani gidan jaru na tsawon shekaru 10 da zargin kisan kai

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Kotun Koli ta Jihar Kwara ta saka wani matashi mai shekaru 21 ga kurkuku na tsaron shekaru 10 akan laifin kisan kai da ake zargin shi da ita.

Shefiu Abubakar zai lashe jarun shekaru 10 ne don kisan dan uwan sa, Babuga Abubakar da bugun itace.

Kotu ta gabatar da shiga kurkukun Shefiu ne a ranar jiya Alhamis 28 ga watan Maris 2019 a jagorancin Alkali Durosinlohun Kawu, a nan Kotun Koli ta garin Ilorin, Babban birnin Jihar Kwara.

Bincike ya nuna da cewa abin ya faru ne a shekarar 2015 da ta wuce a shiyar Dona Dogo ta karamar hukumar Edu, a Jihar Kwara. Ko da shike ba a bayyana dalilin da ya sa aka dakatar da karar har ga wannan lokaci ba, amma an sanya Shefiu da shiga jarun tsawon shekaru 10.

An bayyana ne da cewa Shefiu ya aiwatar da kisan ne da zaton cewa dan uwansa Babuga na kwanci da matar sa.

Ko da shike an fada da cewa Shefiu kamin ya aiwatar da kisan dan uwansa, ya riga yayi karar Babuga ga jami’an tsaron ‘yan sandan yankin da cewa yana zargin sa da kwanciya da matarsa.

Bayan hakan ne Shefiu ya ziyarci gidan Babuga, ya kira shi a waje, ya kuma buge shi da guntun icce, a nan take kuma Babuga ya mutu.

A halin yanzu Shefiu ya riga yayi shekaru hudu a gidan jaru tun lokacin da abin ya faru. Kotu ta bayyana da cewa zai karshe tsawon shekaru shidda don cika sabon hukunci da aka yi masa bisa kan dokar kasa da ya karya.