Connect with us

Uncategorized

Mahara da bindiga sun kai wata sabuwar hari a Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Hari da bindiga a Jihar Kaduna ranar Alhamis 28 ga watan Maris 2019 sun hari shiyar Rigasa, a Jihar Kaduna, inda suka kashe wani mutum da kuma sace matarsa.

‘Yan ta’addan sun fada wa yankin Rigasa da hari ne, suka kuma kashe Malam Abdul’azeez bayan nan suka sace matar tasa kuma. kamar yadda aka baiwa manema labarai.

Abin takaicin ya faru ne missalin safiyar ranar Alhamis da ta gabata a nan unguwar Karshen Kwalta ta yankin Rigasa.

Karanta wannan kuma: Wata ‘yar mace tayi hadarin mota har ga mutuwa a yayin da take kan hanyan zuwa wajen hidimar bautan kasa (NYSC).
Wani mazaunin unguwa guda da Malam Abdul’azeez, ko da shike bai gabatar da sunan sa ba wai don tsaro, amma ya bayyana ga manema labarai da cewa lallai ‘yan hari sun fada wa unguwar su ne da hari suka kuma sace Matan mutumin bayan da suka kashe mijin ta.

“Abdul’azeez Tela ne, yana kuma dinkin Kaftani ne Maza a nan shiyar tamu” inji bayanin mutumin.

Ya kara da cewa Matar Abdul’azeez na da jariri da take baiwa mama, watau ‘nono’ a wannan lokacin da abin ya faru. “Wannan abin ya sanya mu duka cikin wani yanayi a unguwar mu. harin ba mai kyau bane ko kadan” inji shi.

“Muna neman tsaro kwarai da gaske a shiyar mu, hare-hare na kara yawa a kowani rana”

Ya gabatar da cewa sun riga sun yi zana’izar Abdul’azeez bisa ga dokar Islam a bayyanar rana ta ranar Alhamis.

Ko da shike an bayar da cewa ‘yan harin sun yi kira a waya da bukatar a biya wasu kudade kamin su saki matar, amma kakakin yada labarai ga jami’an tsaron ‘yan sandan yankin, Yakubu Sabo, yayi alkawarin cewa zai gabatar da duk wata bayani da ta biyo baya idan ya samu kira daga maharan.