Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 29 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 29 ga Watan Maris, 2019

1. Kotun Kara ta gabatar da kame shugaban Kungiyar Iyamirai (IPOB) Nnamdi Kanu

A ranar Alhamis, 28 ga watan Maris 2019 da ya gabata, Kotun Koli ta Abuja, babban birnin tarayyar kasa, a jagorancin Alkali Binta Nyako, ta gabatar da kame Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ‘yan iyamiran Najeriya (IPOB).

Naija News Hausa ta gane da cewa Malama Binta, a shekarar 2017 da ya gabata, ta bayar da beli ga Nnamdi Kanu bayan wata zargi da ake yi a kansa a wannan lokacin.

2. Buhari ba Kakakin yada labarai ba ne  – inji Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin shugaban kasan Najeriya, ya gabatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ba mai fadi a banza ba ne; “Shugaba Buhari na da muradin kadamar da ayukan kwarai a kasar nan” inji shi.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a wata hidimar murnan karin shekarun haifuwa da shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Bola Tinubu yayi a birnin Abuja ranar Alhamis da ta gabata.

3. Shugaba Buhari ya gabatar da wata sabuwar shiri da ‘yan Fensho

A ranar Alhamis 28 ga watan Maris da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari a birnin Abuja ya ce “Zamu darajanta da Inganta tsohin ma’aikata da suka bauta wa kasar Najeriya”

Shugaban ya gabatar da wata kyakyawar shiri da zai taimaka wa ‘yan fensho don zaman rayuwa bayan da suka yi ritaya daga bautan kasar.

4. Wakilan Jam’iyyar APC sun kaurace wa zaben Gwamnoni a Jihar Adamawa

A ranar Alhamis, 28 ga watan Maris 2019 da ya gabata, Hukumar INEC ta kadamar da zaben kujerar Gwamna ta Jihar Adamawa, kamar yadda ta gabatar a baya.

Naija News Hausa ta gane da cewa Wakilan Jam’iyyar APC sun kaurace wa hidimar zaben, a yayin da sun ki halartan runfar zaben su kamar yadda aka saba yi.

5. Kada Gwamnatin Tarayya ta kara ga biyar kudin harajin kasa – inji Tinubu

Babban shugaban Jam’iyyar APC ta tarayyar kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shawarci gwamnatin tarayya da cewa karin biyan kudin haraji ga ‘yan kasa ba mataki bane mai kyau.

“Karin biyan kudin haraji ga ‘yan kasa ba mataki ba ne mai kyau, zai tsananta wa tallaka ne kawai” inji shi.

6. Ba zamu iya dakatar da Amaechi ba – APC

Jam’iyyar APC sun bayyana da cewa matakin da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya dauka na goyawa dan takara da kumar jam’iyyar AAC baya a Jihar Rivers bai isa su zargeshi da makirci ba.

Kakakin yada yawun Jam’iyyar, Lanre Isa-Onilu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba a wata ganawa.

7. ‘Yan Siyasa, ku bi gurbin Sanata Bukola Saraki – inji INEC

An shawarci ‘yan siyasa da bin gurbin tsohon shugaban gidan majalisar dattijai, Dakta Bukola Saraki.

Hukumar INEC ta gabatar ne da hakan a ranar Alhamis da ta gabata daga bakin Kwamishanan Hukumar na tarayya, Alhaji Mohammed Haruna.

8. Zan tsige Kujerar Gwamna daga hannun Yahaya Bello – inji Mustapha

Mustapha Audu, yaron tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Prince Abubakar Audu, ya gabatar da cewa zai fita takara don tsige kujerar shugabancin Jihar Kogi daga hannun Gwamna Yahaya Bello.

Mustapha ya bayyana hakan ne a wata zamar cashu da ya halarta a garin Lokoja ranar Labara da ta gabata.

9. Hukumar INEC ta gabatar da sabon Gwamnan Jihar Adamawa

INEC a jagorancin Babban Malamin Zaben da ke wakilcin zaben Jihar, Farfesa Andrew Haruna ta gabatar ne da cewa Fintiri ya lashe tseren zaben ne da yawar kuri’u 376,552 fiye da dan adawan sa daga Jam’iyyar APC, Mohammed Jibrila Bindow mai yawar kuri’u 336,386 kasa da kuri’un Fintiri.

Naija News Hausa na da sanin cewa Bindow ne Gwamnan da ke kan jagorancin Jihar kamin wannan hidimar zaben da Fintiri ya lashe, aka kumar gabatar da shi mai nasara ga zaben bisa yawar kuri’u.