Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari na zaman ganawa da Manyan shugabannan Addinan Najeriya

Published

on

at

A yau Jumma’a, 29 ga watan Maris 2019, Shugaba Muhammadu Buhari na zaman tattaunawa da manyan shugabannan Addinai don cin gaban kasa.

A halin yanzu, bisa ga bincike da ganewar manema labarai, shugaban na cikin tattaunawa da shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN).

Zaman ta fara ne da missalin karfe goma sha daya na safiyar yau, a nan cikin fadar gidan majalisar Jihohin kasa ta Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Zaman ganawa da shugaba Buhari da shugaban CAN din ya halarci bayyanar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Ministan Ayukan Waje, Abdulrahman Danbazzau da wasu manyan mambobi da shugabannan kungiyar Kirista ta kasar.

An bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari bayan da ya gama tattunawa da shugaban CAN da mutanen sa, zai kuma gana da Manyan shugabannan Musulunman kasar anan cikin gidan majalisar jihohin a yau Jumma’a.

Duk wata bayani da ya biyo wannan, zamu sanar a nan shafin mu ta Naija News Hausa

Karanta wannan kuma: Karya ce kuri’un da Buhari ya samu ga zaben 2019 – inji Buba Galadima