Uncategorized
Kalli Shawarar da Sanata Saraki ya bayar ga ‘yan Gidan Majalisar Dattijai
Tsohon Shugaban Sanatocin Najeriya, Dakta Bukola Saraki yayi kira ga ‘yan gidan Majalisa da su hada hannu don aiki tare ga ganin cewa sun daukaka kasar Najeriya wajen shugabancin su.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dakta Bukola Saraki ya fadi daga tseren takaran kujerar Sanata daga Jihar Kwara.
Sanata Saraki ya shawarci ‘yan gidan Majalisar ne a yayin da yake wata gabatarwa ga sabbin shugabannin gidan Majalisar ta 9.
“Ku ci gaba da kare zumunci da girman kasar nan Najeriya a duk cikin ayukan ku” inji shugaban a wata bidiyon da ya rabas a layin yanar gizon nishadarwa ta Twitter da ya ke amfani da ita.
Sanata Saraki ya kara da cewa “Yana da muhimanci kwarai da gaske da ganin cewa kan ku na hade. An zabe ku ne daga jam’iyoyi dabam dabam, Idan ko kuna son ku cika gurin ‘yan Najeriya da suka sanya ku a kujerar mulki, dole ne jam’iyyar ku ta zama daya a cikin gidan Majalisar” inji shi.
Karanta wannan: Zaku ko tayar da Hitina, idan har kuka kame Uche Secondus, Sanata Dino ya gayawa Jam’iyyar APC